Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana matsayarsa kan rikicin da ke kunno kai a jam’iyyar APC, musamman dangane da makomar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a zaben 2027.
Zulum ya fadi haka ne bayan rikicin da ya biyo bayan taron APC a Jihar Gombe, inda ake rade-radin cewa ana shirin cire Shettima daga tikitin jam’iyyar a zaben 2027, lamarin da ya janyo martani daga jiga-jigan yankin Arewa maso Gabas.
A cewarsa, “Idan aka cire Shettima daga tikitin jam’iyyar APC, Arewa maso Gabas ba za ta ba da goyon baya ba.”
Gwamna Zulum ya bayyana cewa Shettima shi ne wakilin yankin Arewa maso Gabas a cikin gwamnatin Tinubu, kuma zaɓin sa a matsayin mataimakin shugaban ƙasa ya kasance cikin hikima.
Ya ƙara da cewa APC ba za ta samu nasara a Arewa maso Gabas ba tare da Shettima ba a tikitin 2027, yana mai jan hankalin shugabannin jam’iyyar da su yi taka-tsantsan wajen daukar irin wannan mataki.
Zulum ya ce irin wannan yunƙuri na iya haifar da rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar APC da kuma ƙarfafa siyasar “mu da namu” a yankin.
KU BIYO MU A FACEBOOK