Daga Abdullahi Alhassan.
Wata mai neman tsayawa takarar kujerar Shugaban Karamar hukumar Kajuru a Jihar Kaduna, Barista Esther Ashiven Dawaki ta lashi takobin samar da tsaro a Karamar hukumar,tare kuma da karfafa Mata da Matasa don dogaro da kansu,
Barista Esther a baiyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai, jim kadan bayan sayan fam din nuna sha’awarta na tsayawa Takarar Shugaban Karamar hukumar Kajuru,a nan Jihar Kaduna,
Misis Dawaki, tace al’ummarta ne suka bata kwarin gwiwar fitona Takarar,ganin yadda take kulawa da su mussammam ma lokutan da suke da bukatar taimakon ,na ganin ansamar musu da tsaro a Karamar hukumar mai fama da hare haren yan bindiga wanda ke kawo asaran Rayukan al’ummar,
Ta kara da cewa tuni take cigaba da lalubu hanyar magance matsalar inda tace zatayi aiki da Jami’an tsaro don basu kayan aikin don tunkarar matsalar da kuma maganceta,
Barista Esther ,ta kuma cigaba da cewa abu na gaba shi ne samar da aikin yi ga Mata da Matasa don dogaro da kansu ganin cewa Gwamnati bazata lya daukar kowa aiki ba,to amma zamu hada kai da hukumar koyar da Sanaoi don koyawa Mata da Matasan mu don rage dogaro da aikin Gwamnati kawai ,akwai tsari da mukayi na ganin an talafama musu da jari koda babu yawa hakan zaisa su zama masu dogaro da kansu,
Daga karshe ta nemi hadin kan yan Karamar hukumar don ganin sun bata hadin kai da goyan baya don cimma burin da tasa a gaba na kyautata Rayuwar al’ummar Karamar hukumar in Allah yasa ta zama Zababiyar Shugaban Karamar hukumar a zabe mai zuwa