Za a yi wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo allurar rigakafin of AstraZeneca/Oxford ranar Asabar mai zuwa.
Babban daraktan hukumar ba da lafiya a matakin farko na kasar Dakta Faisal Shuaib ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja.
A cewarsa wannan matakin zai karawa ‘yan Najeriya karfin gwiwar su fita a yi musu rigakafin da aka kai kasar a wannan makon.
“Akwai shirin fara yi wa jami’an lafiya da ke kan gaba wajen yaki da cutar,” in ji Dakta Faisal
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER