UWAR JAM’IYYAR APC TA KARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA TA AMSHI DR SURAJO YAKUBU BATAGARAWA YAU LAHADI 4/4/2021,,,
________________
Uwar Jam’iyyar Apc ta karamar Hukumar Batagarawa ta amshi Dr Surajo Yakubu Batagarawa, Wanda Yabaro Jam’iyyar PRP Wadda shine Legal Adviser dinta a matakin Kasa Baki daya,,,,
A Jawabinsa Shugaban Jam’iyyar Apc Na karamar Hukumar Batagarawa Alh Bala Garba Tsanni Yache Jam’iyyar tayi Babban kamu domin koba komai Dr Surajo a matsayinsa na Dan karamar Hukumar Batagarawa Kuma Wanda yake rike da Babbar Kujera a Jam’iyyar PRP amatakin Kasa Baki daya Mutum ne Jajirtache,,,
Yau gashi yazabi yadawo Jam’iyyar Apc Mai Albarka,, Alh Bala yayi Kira ga Ya”Yan Jam’iyyar Apc Na karamar Hukumar Batagarawa Dana mazabu musamman Mazabar Batagarawa ward A, dachewa Ga Dr Surajo Nan Dane Kuma Kane ne, sannan Kuma Abokinku ne, Alh Bala Garba ya Tabbatar wa Dr Surajo Chewa a Shirye suke dasu bashi goyon baya a duk Lokachin da yabukachi hakan Kuma zasuyi Tafiya dashi busa ga Amana madamar Ya kasanche Mai Biyayya ga Jam’iyyar Apc tundaga matakin Mazabu na ward Dana karamar Hukuma da jaha da kasa Baki daya,
Anashi jawabin Aboki kuma Aminin Dr Surajon Watau Haruna Usman Batagarawa yabada Dan takaitachen Tarihin Dr Surajo Yakubu, inda Yache An haifeshi a karamar Hukumar Batagarawa, Kuma yayi primary Dinsa da karamar sakandire Dinsa a Garin Batagarawa, a takaiche dai yache Dr Surajo yakubu Batagarawa, Yayi Digirnsa na farko Dana biyu Dana Uku a kasar Engla a fannin Shari’a, Kuma yayi aiki a Lokachin Mulkin Marigayi Umar Musa Yar’adua a Villa, Yakasanche Daya daga chikin Jami’an tsaro na farin Kaya a ofishin Mataimakin Shugaban kasa a Lokachin,
A Jawabinsa na Godiya Dr Surajo yakubu yayi Godiya ga Al’ummar dasuka samu damar Halartar wannan Bikin Karbartasa tundaga matakin Exco na ward Dana Karamar Hukuma,
Dama sauran jama’a musamman Matasan da yagani a gurin Taron, Kuma yayi Alkawarin chewa zai zamo Mai Biyayya dakuma Bin doka da Order ga Jam’iyyar Apc da Al’ummar Daya yasama achikinta masu Albarka.