An yi awon gaba da shugaban kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC, Kwamared Ben Ukpekpi.
A cewar rahotanni da ke zuwa DAILY EPISODE HAUSA, an sace Ukpekpi yayin da yake tsaye a gaban gidansa da ke CROSPIL Estate, Akpabuyo, a wajen garin Kalabar tare da matarsa da misalin karfe 8 na daren ranar Lahadi, 21 ga Maris, 2021.
Masu garkuwan sun dauke shi ta cikin kogin da ke kan gadar da ke Atimbo.
Da sauri dan Ukpekpi ya shiga mota ya bi su a baya. Masu garkuwar sun harbi tayoyin motar kuma sun fashe tayoyin.
Ba a san inda shugaban ya ke ba tunda har yanzu masu garkuwan ba su tuntubi dangin don neman kudin fansa ba.
Wannan shi ne karo na biyu da za a sace Kwamared Ukpekpi a gaban gidansa bayan lamarin na farko a watan Disambar 2019.