Rahotannin da mu ke samu daga Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata kusan 300 daga makarantar sakandiren GSS Jangeɓe da ke jihar da tsakar daren Juma’a.
Mahaifin daya daga cikin daliban da kuma wani malami da ke makarantar lokacin da aka sace daliban ya tabbatar wa BBC aukuwar lamarin.
Har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar da ma gwamnatin Zamfara ba su ce komai a kan batun ba.
Wannan na zuwa ne yayin da ake kokarin kubutar da daliban makarantar sakandiren Kagara da malamansu da yan bindiga suka sace a jihar Neja.
Jihar Zamfara na cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren ‘yan fashin daji da masu satar mutane domin karbar kudin fansa.
Muna ci gaba da samun ƙarin bayani a kan wannan labari na Zamfara, za mu sanar da ku ci gaban da aka samu…