Tsohon kakakin shugaban kasa a zamanin mulkin Goodluck Jonathan da kuma Olusegun Obasanjo, Doyin Okupe ya tabbatar da cewa akwai Aljanu a fadar shugaba kasar ta Aso Rock.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a jaridar Vanguard inda yace amma fa aljanun ba daga cikin fadar suke ba.
A baya ma dai Tsohon hadimin shugaban kasa, Reuben Abati ma ya tabbatar da cewa, Akwai Aljanu a fadar shugaban kasar ta Aso Rock.
Okupe yayi dariya da aka masa tambayar amma yace, maganar gaskiya daga kauyuka da jihohi Aljanun suke fitowa.
KU BIYOMU A FACEBOOK DA TWITTER