Gwamnan jihar Zamfara, Mista Bello Matawalle, a jiya ya ce ‘yan Nijeriya za su yi mamakin sanin wadanda suka sace daliban mata 317 na Makarantar Sakandaren’ Yan Mata ta Gwamnati, Jangebe.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da Sarakuna 17 a jihar suka kai masa ziyarar ta’aziyya kan sace ‘yan matan makarantar.
A yayin ziyarar, Sarkin Anka kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, Alhaji Attahiru Anka, ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kara kaimi wajen magance yawaitar kashe-kashe da sace-sacen mutane da ’yan fashi ke yi a kasar.
A nasa jawabin, Matawalle ya gode wa sarakunan bisa wannan hadin kai da ya kawo musu, ya kuma ba su tabbacin cewa ba zai yi watsi da yarjejeniyar zaman lafiya da ya yi da ‘yan ta’addan ba ko da kuwa menene mutane za su ce.
Ya ce “Yayin da muke jiran sakin daliban GSSS Jangebe da aka sace a gidan Gwamnati a yau, ina so in sanar da ku cewa akwai bayanai da yawa dangane da sace wadannan daliban.”
“Mutane da yawa za su yi mamakin jin wadannan mutane a bayan sace wadannan yara marasa laifi.”
“Ba su da kwanciyar hankali game da ci gaban da nake samu sakamakon kudirin na zaman lafiya kuma suna son yin duk abin da za su iya yi wa kokarin na zagon kasa”.
“Zan yi nasara insha Allah a ƙarshen rana kuma za su rufe fuskokinsu cikin kunya,” in ji gwamnan.