- Yan matan da aka sace na makarantar kwana ta GGJSS Jangebe an haura dasu dajin Dangulbi – Ganau
Yan matan da aka sace na makarantar kwana ta GGJSS Jangebe an haura dasu dajin Dangulbi – Ganau
Wasu ganau ya bayyana cewa ya hangi yan matan sakandare na karamar sakandare ta kwana ta kuma yan mata zalla da yan bindiga suka shiga garin Jangebe karamar hukumar Maru jihar Zamfara suka sace a daren jiya Jumu’ah suna dajin Dangulbi
Za a iya tuna cewa rundunar yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da cewa dalibai Yan Mata 317 ne yan bindigar suka gudu da su, masu shekaru daga 12 zuwa 16.
Sai dai kwamishinan tsaron jihar Zamfara ya bayyana cewa har yanzun ba su ida tantance cewa ko dalibai nawa ne suka bace ba.
Amma wani malami a makarantar ya tabbatar wa majiyarmu ta Daily Trust cewa makarantar tana da dalibai sama da 600, amma wadanda aka samu ba su wuce 50 ba.
Sace daliban na zuwa ne bayan da yan bindiga suka sace daliban makarantar GSSS Kagara jihar Niger da har zancen da ake ciki yanzun ba a sako su ba, Kamar yadda Katsina Daily Post News ta rawaito maku labarin a wannan shafin kwanakin da suka wuce.
Sai dai shugaban kasa Buhari ya ce Gwamnati ba za ta yarda da barazanar yan ta’ada wajen ganin ta sami kudi da Gwamnatin don biyan kudaden fansa ga daliban da suke sacewa, don haka kar su dauka cewa sun fi karfin Gwamnati, kuma za a ceto dukkanin daliban ba tare da salwantar rayuka ko jikkata ba.
Wasu ganau ya bayyana cewa ya hangi yan matan sakandare na karamar sakandare ta kwana ta kuma yan mata zalla da yan bindiga suka shiga garin Jangebe karamar hukumar Maru jihar Zamfara suka sace a daren jiya Jumu’ah suna dajin Dangulbi
Za a iya tuna cewa rundunar yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da cewa dalibai Yan Mata 317 ne yan bindigar suka gudu da su, masu shekaru daga 12 zuwa 16.
Sai dai kwamishinan tsaron jihar Zamfara ya bayyana cewa har yanzun ba su ida tantance cewa ko dalibai nawa ne suka bace ba.
Amma wani malami a makarantar ya tabbatar wa majiyarmu ta Daily Trust cewa makarantar tana da dalibai sama da 600, amma wadanda aka samu ba su wuce 50 ba.
Sace daliban na zuwa ne bayan da yan bindiga suka sace daliban makarantar GSSS Kagara jihar Niger da har zancen da ake ciki yanzun ba a sako su ba, Kamar yadda muka samu labari ta rawaito maku labarin a wannan shafin kwanakin da suka wuce.