Ma’aikatan jami’ar Greenfield da daliban da aka sace sun sami ‘yanci kwanaki bayan sace su.
Ku tuna cewa Daily Episode ta rahoto cewa an yi garkuwa da ma’aikata da daliban jami’ar Greenfield a ranar 20 ga Afrilu 2021 a harabar makarantar da ke Kauyen kasarmi da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
‘Yan fashin sun kashe dalibai biyar yayin da ma’aikacin jami’ar shi ma aka kashe yayin garkuwar.
An saki ma’aikatan da daliban bayan sun biya kudin fansa sama da miliyan dari da hamsin da babura ga ‘yan fashin.
Dalibin da ma’aikatan sun sake haduwa da yan uwansu da danginsu bayan an sako su daga garkuwar.
Wasu daga cikin iyayen na nuna farin ciki yayin da suke kuka da gazawar gwamnati wajen tsare rayukan yaransu da aka sace.
Gwamnatocin jihar ta Kaduna sun kuma tabbatar da sakin daliban da ‘yan bindigan suka sace a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin tsaro, Mista Samuel Aruwan.
An tura iyaye, ma’aikata da ɗalibai zuwa wurare daban-daban da hawayen farin ciki.