Al’ummar garin Ruwan Tofa na yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya, sun gamu da taskun ‘yan bindiga, wadanda rahotanni suka ce sun kona rabin garin da dukiya mai dimbin yawa, kuma suka yi awon gaba da mutane fiye da sittin.
Hakan ya auku ne yayin da matsalar satar ‘yan makaranta ta fara auka wa daliban makarantun jeka-ka-dawo a garin Runka na jihar Katsina.
madogara: BBC