Yan bindiga sun kai hari ofishin ‘yan sanda da ke Abayi a Aba a ranar Talata. Makonni bayan ƙona ofihsin ‘yan sanda na karamar hukumar Isiala-Ngwa ta Kudu da ke jihar Abiya a Kudu maso gabashin Najeriya.
Jaridu a Najeriya na rawaito cewa ‘yan bindigar sun kashe wani dan sanda mai mukamin ASP da kuma wani kurtu a harin.
Sun kuma rawaito cewa da misalin karfe 2:30 na dare ne maharan suka kai harin tare da satar makamai su gudu da su.
Wannan lamari dai ya kara haifar da zaman dar-dar a fadin jihar, abin da ya sanya ‘yansanda gudanar da ayyukansu cikin fargaba.