Rahotannin dake shigowa manema labarai ta hanyar Matar wanda aka kashe tace; wadansu ‘yan bindiga sune suka kashe Maigidan na ta wanda kafin a kashe shi shi ne magatakardar Hukumar shirya jarabawar kammala Sakandare ta kasa, NECO, wato Farfesa Godswill Obioma.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai masa hari ne a daren ranar Litinin a gidansa, inda suka shake shi wanda matarsa ta bayyana kisan na shi a matsayin kisan kai.
Da safiyar yau Talata ne matarsa, Elizabeth Obioma ta shaidawa manema labarai ta wayar tarho cewa wadanda suka kashe mijin na ta ba su dauki komai ba bayan sun kashe shi.
“Masu kisan kai din sun shigo ne kawai suka kashe shi suka tafi ba tare da daukar komai ba”, ta tabbatar.
Elizabeth Obioma wacce ta rika bada labari cikin matsanancin kuka, ta tabbatar da cewa mijinta bai jima da dawowa daga Minna ba bayan wata ziyara da ya kai Abuja, sai ga shi kwatsam ‘yan bindigar sun shigo gidansa sun kashe shi.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Neja, ba ta dauki kiran wayar da majiyarmu ta yi mata ba. Farfesa Godswill Obioma dai a kwanakin nan ne aka ayyana dakatar da shi daga mukaminsa na shugaban Hukumar NECO.