Taimakakon marayu da marasa Karfi na Daya daga cikin manyan ayyukan alkhairi da ake so al’umma su yawauta yin su.
Hakan ne ta sa Malama Fatima Adam Ismail ta tashi tsaye wajen Samar da wata cibiya da ke a gundumar Rigasa na karamar hukumar Igabi ta Jahar kaduna, don samarwa irin wadan nan Yara (Marayu) ilimi da Kuma koya musu sana’oi dogaro da kai kyauta.

Kokarin ta na inganta rayuwar yaran nazuwa a daidai kan gabar da Dinkin Duniya Tafitarda kididdgar yawaitar yara kanana marasa zuwa makaranta ya haura kimanin yara millian ashiri, kididdgar da ta nuna cewar akalla acikin yara daya daga cikin yara goma da basa zuwa makaranta a duniya ‘yan najeriya ne.
Dukda cewa gwamnatin tarayyar Najeriya da Kuma na jahohi sun mike tsaya wajen shawo kan matsalar ta hanyar fitar da tsare tsare dakuma ware makudan kudade don kashewa bangaren illimi a fadin kasar.
Saidai wancan muradu na gwamnatin Najeriya da kuma burin da ta ke shi akan ilimi zai samu nasara idan aka samun yawaitar masu kokari a cikin al’umma irinsu Malama Fatima da sauran kunguyiyi da ke taimakama bangaren illimi da al’umma Baki daya.
Kamar yadda jaridar Daily Episode ta tattaro daga bayanan malama Fatima, akwai yara marayu da Kuma wadanda iyayen su Basu da karfi akalla guda sittin da bakwai da ke karatun kyauta a karkashin kulawarta, da kuma taimakon wasu bayin Allah.
Wanda sakamakom wanan taimakon ya sa al’umma da dama ke tururuwan zuwa naiman taimako a wajenta.

A cewar ta, “yanayin da yara kanana keshiga sakamakon rashin zuwa makaranta yasa ni jajircewa wajen inganta rayuwar su, wanda hakan ya haifar da kungiyar Zam-zam foundation daga bisani kuma Allah yabamu damar bude makaranta mai suna Adam Bin Mahmud”.
“Idan muka lura acikin shekarun nan, illimi na ci gaba da samun koma baya, a sakamakon karancin gata ko rashin hali wanda ke kawo tsaiko ga karatun yara musanman ‘ya’ya mata da ake kaiwa aikatau ko yawon tallace-tallace ko kuma aurar da su da ake yi ba tare da sun samu isashen ilimi zaman sa ba”.
Kuma ni nafi ganin alfanun iyaye su dage wajen bawai ‘ya’yan su illimi sabida sune manyan gobe kuma tarbiya za su yi wa ‘ya’yan su, idan basu samu isashen ilimi ba, taya za su san alfanunshi kuma subada tarbiya mai inganci?.”
Malama Fatima ta ci gaba da cewa “bawai iya ‘ya’ya matane kadai yadace akai makaranta ba, domin yaya maza ma sunfi shiga hadari sakamakon rashin ilimi da kuma barin gidajen iyayen su abcikin karancin shekaru a wanan zamanin”.
“Dukda cewa wasu ana kaisu alamajirci, shima kuma yana tauyesu tafannin rashin samun ilimin zamani, da kuma sanadin duba da kyara da rashin baiwa almajirai dama da kowane bangare keyi”.
“Za ka samu yawan cin yaran da ke yawo babu ilimi ko sana’a wasu nada iyaye, wasu kuma marayu ne anma yan uwanbsu sunbar su haka, wanan ya za ma wajibi mudage domin gina rayuwar su kafin sufi karfin mu.
Idan kaduba, mu azamaninmu ‘ya’ya mata basa zuwa boko sabida iyayen mu ba su gamsu da karatunba, anma yanzu yazama wajibi”.
“Idan ban mantaba, wanan dalilin ne yataka rawar gani wajen bude makarantar nan tamu, kuma cikin ikom Allah gashi har an shekara, kuma karatu na ci gaba na boko da kuma na addini”.
Da ta ke jawabin bangajiya wajen taron cika shekara daya da makarantar ta Adam Bin Mahmud ta shirya, Malama Fatima ta yiwa Allah godiya ta re da mika sakom godiya ga al’umma bisa irin goyon bayan da suke baiwa makarantar don ganin ta inganta rayuwar yaran.

Taron dai ya samu halartar manyan Baki ciki harda baban malamin addinin musulunci Sheikh Dr Ahmad Gumi inda ya ja hakalin jama’a don dagewa wajen bawai ‘ya’yan su ilimi, ganin yadda ya ke taka rawa a rayuwar duniya da lahira.
A cewarbsa, yazama wajibi a dukufa wajen inganta rayiwar yara da kuma tsaron al’umma ta hanyar bada ilimi mai inganci.