Wata mata mai suna Amina ta lakadawa Kishiyarta Fatima duka har lahira sannan ta cinnawa gawarta wuta a Minna, jihar Neja.
Al’amari yafarune a Mandela road mina , jihar Neja.
An ce mummunan lamarin ya faru ne a ranar Talata, kwanaki hamsin bayan bikin Fatima.
Jaridar Daily Daily ta tattaro cewa, matan biyu ba sa zama a gida daya.
Duk da basa zama a gida daya, Matar farko da yan uwanta sun mamaye gidan wanda aka Fatima don aikata laifin.
Ana saran yin janaizar Fatima a ranar Laraba a Sabuwar Unguwa a jihar katsina.
Rundunar ‘yan sandar jihar Neja ta samu nasarar cafke wanda ake zargin a mina.