- Afendis wato “appendid” a turance, wani dan zunbutu ne mai kamar jela a mahadar karamin hanji da babban hanji. Girmansa yai kama da girman yatsan hannu.
- A ina afendis yake? Afendis yana nan a ciki a kwibin dama daga kasan cibiya kadan.
- A likitance, afendis ba shi da wani takamaiman aiki a jiki dan Adam. Sai dai wasu masanan na cewa afendis na dauke da wasu kwayoyin garkuwar jiki.
- Ciwon afendis wato “appedicitis” a turance, ciwo ne a afendis sakamakon kumburin afendis saboda wasu dalilai.
- Abubuwan da kan haddasa kumburin afendis sun hada da: harbin kwayoyin cuta kamar bakteriya, toshewar bakin afendis daga dunkulallen turbayan abinci ko kashi, ciwon daji/sankara da sauransu.
- Alamun ciwon afendis sun hada da:
– ciwo a kwibin dama kasa da cibiya kadan.
– ciwo a kewayen cibiya wanda daga bisani kan zarce zuwa kwibin dama.
– ciwon da ke ta’azzara yayin tari ko wani yunkuri.
– ciwo yayin da aka danna kwibin dama da cibiya.
– tashin zuciya da amai.
– Rashin sha’awar cin abinci.
– matsakaicin zazzabi, da sauransu.
7. Ciwon afendis na bukatar tiyatar gaggawa domin cire shi, musamman idan ya riga ya fashe ko kuma ana tsoron fashewarsa a kowanne lokaci.
8. Barin ciwon afendis ba tare da an cire shi ta hanyar tiyata ba na da hadarin gaske, domin fashewarsa na nufin fantsamar kwayoyin cuta da ke kunshe ciki zuwa dukkan sauran kayan ciki.
9. Hanyar kariya daga ciwon afendis: babu wata sahihiyar hanyar kariya daga ciwo afendis; sai dai masana kimiyyar abinci na ganin cewa ciwon afendis bai cika kama masu cin datsar hatsi, gayayayaki da ‘yayan itatuwa ba – wato masu kaurace wa sarrafaffen abinci kenan.
10. Yaushe ya kamata ka ga likita? Da zarar ka fara jin wasu daga cikin alamun da aka ambata a sama garzaya asibiti domin duba ka.