Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, zai kai ziyara jihar Zamfara domin kaddamar da muhimman ayyuka da gwamnatin jihar ta kammala.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce tsohon shugaban zai kaddamar da Asibitin Kwararru na Yeriman Bakura, wanda aka gyara gaba ɗaya tare da samar masa da kayayyakin zamani.
Haka zalika, Obasanjo zai kaddamar da wasu manyan tituna da ke unguwar GRA a Gusau, wadanda ke cikin jerin ayyukan sabunta birnin da gwamnatin jihar ke aiwatarwa.
KU BIYO MU A FACEBOOK