Abubakar Ismail Kankara
Rahotanni da muka samu sun nuna cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu don cigaba da aikin hakar man fetur a Kalomi dake Jahar Bauci.
Ministan Albarkacin mai na kasar, Heineken Lokpobiri ne ya bayyanawa manema labarai a cikin wata sanarwa da mista Nneamaka Okafo dake taimakawa ministan kan harkokin sadarwa ya fitar a jiya lahadi 18 ga watan Mayu.
Bayann sun tabbatar cewa shugaban kasa yabada izini da kuma dukan lasisi don cigabada aikin ba tareda tsaiko ba.
Ministan ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya karkashin shugaba Tunubu ta samar da cibiya ta musanman wace take nazari don kawo sauyi da kuma hana tsaiko don cigaban aikin.
tun a shekara 2022 ne di aka fara wanan aikin a karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari tun bayan da aka bada damar fara aikin a Kalomidon bunkasa tattalin arzikin Najeriya.