Hukumar zabe ta kasa ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na jamiyyar APC mai mulki a matsayin wanda yayi nasara lashe zaben shugaban kasa, biyo bayan kanmala alkaluman zabukan shugaban kasa da na majalisun tarayya Najeriya na shekarar 2023 da ya gudana a fadin kasar.
Shugaban hukumar zaben na kasa, farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da nasar Bola Tinubu a shelkwatar tatara alkaluman zabe dake birnin tarayya Abuja da misalin karfe hudu na asubar ranar laraba.
A nasa jawabin, Farfesa Mahmood Yakubu yace, tsohon gwaman jahar lagos din yasami kuri’u miliyan 8,794,726 a fadin kasar.
Hakan yaba Bola nasar akan me bi masa a yawan kuri’a wato Alhaju Atiku Abubakarna jamiyyar PDP kuri’u miliyan 6,984,520.
Kazalika, Peter Obi na jamiyyar labour Party ya sama kuri’u miliyan 6,101,533 wanda ya dara Rabi’u Musa Kwankwaso na jamiyyar NNPP wanda ya sama kuri’u miliyan 1,496,687.