Yayin da Ayyukan Ta’addanci ke Karuwa a Arewa Maso Gabashin Najeriya, Sojojin Operation Hadin Kai Sun Kaddamar da Hari Mai Tsauri Kan Sansanonin Boko Haram da ISWAP
Sojojin Najeriya a karkashin Operation Hadin Kai sun kai wani mummunan farmaki ta sama da kuma kasa a safiyar Litinin, 9 ga Yuni, 2025, kan sansanonin ‘yan ta’adda a Nzalgana (karamar hukumar Gujba) da kuma Tumbuktu Triangle da aka sani da zama maboyar ‘yan ta’adda.
A cewar sanarwar da rundunar sojin Najeriya ta fitar:
“A safiyar yau, 9 ga Yuni, 2025, dakarun Operation Hadin Kai sun kai hari ta sama da ta kasa lokaci guda kan sansanonin Boko Haram/ISWAP da ke Nzalgana, Gujba LGA, da Tumbuktu Triangle, wanda ya haifar da babban asara ga ‘yan ta’adda da shugabanninsu. Musamman, an kashe Ameer Malam Jidda, daya daga cikin kwamandojin manya da ke jagorantar ayyukan ta’addanci a kauyukan Ngorgore da Malumti. Haka kuma, a Abadam, an gano karin gawarwakin ‘yan ta’adda da makamai bayan wani samame da aka gudanar a Mallamfatori.”
Majiyoyin soja sun tabbatar da cewa Ameer Malam Jidda, wanda aka fi sani da shugaba mai kisa a yankin Ngorgore da Malumti, yana daga cikin wadanda aka kashe a wannan hari. Wasu da dama daga cikin mayakan boko haram din da aka kashe, yayin da wasu da yawa suka samu munanan raunuka.
A wani hari dabam da aka kai a Abadam, dakarun sun gano karin gawarwaki da tarin makamai bayan da suka kammala sintiri a Mallamfatori, wanda aka sani da zama wata hanya da kuma cibiyar kayan aikin ‘yan ta’adda.
Rundunar sojin Najeriya ta jaddada kudirinta na kawar da dukkanin ‘yan ta’adda da dawo da zaman lafiya a yankin.
KU BIYO MU A FACEBOOK