Sojojin rundunar Operation Hadarin Daji sun hallaka ’yan ta’adda shida a wani artabu da ya faru a karamar hukumar Gudu, Jihar Sakkwato.
Daraktan Yada Labarai na rundunar, Laftanar-Kanar Abubakar Abdullahi, ya ce an kwato bindigogi kirar AK-47 guda hudu da harsasai 160 nau’ika daban-daban daga hannun ’yan ta’addan.
Sai dai, ya bayyana cewa rundunar ta rasa sojoji biyar a yayin wannan musayar wutar. Ya kuma bukaci al’umma da su kasance masu lura da kai rahoto kan duk wani motsi da ba su yarda da shi ba.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA X