Yayin da arewacin Najeriya ke fama da karuwar ta’adancin ‘yan fashi da garkuwa da mutane, rundunar sojin saman Najeriya ta dakile harin da wasu ‘yan ta’adda na ‘yan bindiga suka kai a makarantar horas da sojoji ta Najeriya wato NDA
A cewar wani rahoto da kafar yada labarai ta PR Nigeria ta wallafa, an kawar da ‘yan ta’adda kusan 20 a ranar Alhamis yayin da suke tserewa domin gujewa harin bama baman sojojin saman Najeriya.
Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan sun tunkari cibiyar horas da sojoji kimanin su 50 a kan babura tare da shirin sake kai harin da suka samu nasara a bara.
Ku tuna cewa Daily Episode ta ruwaito yadda ‘yan bindiga suka kai hari makarantar horas da sojoji ta Najeriya, NDA, kuma suka yi garkuwa da wasu jami’an soji tare da kashe wasu.
Jihar Kaduna dai ta kusa tabarbare a fannin tsaro a ‘yan kwanakin nan ganin yadda yankunan Arewa, Gabas, Yamma, da Kudancin jihar ke fama da tashe-tashen hankula a harkokin tsaro tare da yawaitar sace-sacen mutane, kashe-kashe, satar shanu, da rikicin addini da na kabilanci.
Wani Bakon Kisan Da Aka Yi Wa Manajan Kaduna
Hankalin Jama’a ya tashi a jahar Kaduna ranar Juma’a, yayin da aka kashe wani babban ma’aikaci mai mukamin Darakta ayyuka na Kaduna Geographic Information Service (KADGIS), a gidansa mai iyaka da sansanin sojojin saman Najeriya da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Daily Episode ta tattaro cewa wasu makasa sun samu shiga gidan marigayin da ke Barakallahu GRA, karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna, domin aiwatar da kisan.
Alhaji Ibrahim Gaya, mazaunin unguwar kuma shugaban al’ummar garin Barakallahu GRA, ya bayyana kaduwarsa da faruwar lamarin, inda ya koka da cewa duk da kokarin da suke yi wajen tabbatar da tsaro a unguwarsu da muhallinsu, anma wasu mahara sun karya yunkurinsu na kashe wani mutum mai muhimmanci, wanda ya amfanar da al’umma da jihar kaduna.
Muna fatan jami’an tsaro za su gano wadanda suka aikata wannan kisan gilla domin ba a sace kowa ba, ba a kuma sace dukiya ba; masu laifin kawai sunzo ne don su dauki ran Dauda ne kawai.
Sai dai ya bukaci gwamnatocin tarayya da na jihohi da su kara inganta tsaro a kasar nan, musamman na kananan hukumomin Igabi da Giwa, da ke kara samun karuwar laifukan da suka shafi ‘yan fashi, yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Sai dai an binne marigayin ne a mahaifarsa, Anchau, kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada.
Maharan sun kuma yi hanyarsu ta zuwa tsohon barakallahu, inda suka afka wani gida na wani Bitrus Gajere, suka yi awon gaba da wasu kayayyaki masu daraja.
Fira da wadanda iftila’in ya afkamawa
Mista Bitrus ya bayyana cewa masu barayin sun harba bindiga sau biyu a cikin gidansa, suka fasa dakin dansa kuma suka sace wayoyi, kwamfutar tafi-da-gidanka, da kuma jakar dansa.
Mun gode wa Allah da babu wanda aka jikkata ko aka yi garkuwa shi, amma mun firgita kuma mun yi hasarar dukiya sakamakon abin da suka dauka.
Patience Joel ta ba da labarin yadda suka boye sa’ad da suka ji ƴan ta’addan na ƙoƙarin yin kutse da shiga ɗakinsu ta taga.
addu’a mukayi kuma muka ɓuya a wurare daban-daban. Mun jin su a lokacin da suka shigo, amma ba su same mu ba, sai suka kwashe abin da suke so.
Ba mu iya barci ba saboda harbin bindigar ya yi nauyi tareda tsorata mu.
Patience ta kuma yi kira ga gwamnati da ta taimaka wajen samar da tsaro ga al’ummarsu domin kare rayukan su da dukiyoyinsu.
Yayin da ake hada wannan rahoto, hukumomin ‘yan sanda ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.