">
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
Thursday, October 16, 2025
No Result
View All Result
NEWSLETTER
Daily Episode Hausa
-18 °c
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
No Result
View All Result
Daily Episode Hausa
No Result
View All Result
">

SHEIKH IBRAHIM INYASS (RH)

by Abubakar Ismail kankara
January 25, 2025
in Addini
0
SHEIKH IBRAHIM INYASS (RH)
Share on FacebookShare on Twitter
">

RelatedPosts

ABUBUWA 13 DA SUKE LALATA AURE

Tasirin Taimako: Hanyoyin Da Zai Tabbatar Da Ci Gaban Al’umma

">

Daga: Aliyu Dahiru Aliyu

A duk lokacin da kaga wani mutum mutane sun rabu gida biyu a kansa, tsakanin mai kambamashi har ya kaishi matsayin allantaka da kuma mai zaginsa ya mayar da shi tamkar shedan; ka tabbatar akwai ababan izina a rayuwar wannan babban mutum da ya kamata a lura da shi duba na tsanaki.

Sheikh Ibrahim Inyass ya rabu gida biyu a gurin musulmin yammacin Afrika tamkar yadda Sayyidi Ali ya rabu tsakanin “ghullatus Shi’a” masu allantar da shi da kuma Banu Umayya masu zaginsa. Tamkar Annabi Isa (as), tsakanin yahudawan da suka yi zaton sun kasheshi da kuma kiristocin da suka allantar da shi.

Wani abu da ya janyo mutane suka rabu gida biyu a kansa yana da alaka da yanayin kalaman sufancin da yake da salon irin su Abu Mansur Alhallaj da kuma Sheikhul Akbar Ibnul Arabiy da mutane suka rabu a kansu, tsakanin masu ganinsu a manyan zindikai da kuma masu daukansu manyan waliyyai. Haka kuma maganganun manyan litattafan da suke dadewa a tarihi suke cike da tauriyyar da mutane suke yi musu fahimtu mabanbanta.

Alqur’ani, Bible, Torah da Vedas sun dade a tarihi ne kuma suna daukan mabanbanta zamani da mabanbantan guri saboda suna daukan sharhi da fassara daidai juyawar zamani. Da litattafan sun yi magana zallanta da ba wani surkuki a ciki da canjin zamani zai tafi da su ne. Alqur’ani a misali zaka tarar yana fuskoki dayawa ta yadda kowa yake da fassararsa ta daban akai. Masu neman zaman lafiya da yan ta’adda kowa gani yake Alqur’ani goyon bayansa yake!

A takaice dai Sheikh Ibrahim Inyass zai dade tarihi bai manta da shi ba. Kuma zai tafi tsakanin masu ganinsa malami kawai da masu ganin shi allah ne baki daya! Wasu kam kallon shedan za su dinga yi masa. Rayuwar Sheikh Ibrahim irin ta manyan mutanen da ake rarrabuwa akansu ce. Kowa da fuskar da yake ganinsa. Wannan ta sa Sheikh Ibrahim ya zama babban mutum.

Yardarka da Shehu Ibrahim ita tasa ya zama babban mutum. Rashin yardarka da shi ita ta kara tabbatar da babban mutum ne. Tarihi zai dade yana ambatonsa.

">
Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail Kankara is the founder and CEO of AIACCESS Contractors and the Managing Editor OF Daily Episode

Related Posts

ABUBUWA 13 DA SUKE LALATA AURE

ABUBUWA 13 DA SUKE LALATA AURE

by Abubakar Ismail kankara
January 28, 2025
0

Rubutun: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa  1.KISHI MAI TSANANI. Idan kishi ya yi tsanani da yawa sai ya zama matsala ga...

Ci Gaban Al’umma

Tasirin Taimako: Hanyoyin Da Zai Tabbatar Da Ci Gaban Al’umma

by Abubakar Ismail kankara
January 25, 2025
0

Rubutun: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa  Taimako na kowane fanni yana da muhimmanci sosai wajan ci gaban al’umma, domin yana haifar...

Next Post
Ci Gaban Al’umma

Tasirin Taimako: Hanyoyin Da Zai Tabbatar Da Ci Gaban Al’umma

Rashin Fahimtar Aiki: Martani kan Rikicin AKTH da Berekete Family

Rashin Fahimtar Aiki: Martani kan Rikicin AKTH da Berekete Family

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

">
  • Talla
  • Tuntube Mu
  • Gida
TUNTUBE MU: 08032398985 info@dailyepisode.ng

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

Login to your account below

Forgotten Password?

Fill the forms bellow to register

All fields are required. Log In

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In