A dai-dai lokacin da ake fama da yawan yaran da basa zuwa makaranta musamman a fadin arewacin kasar nan, mai martaba sarkin rano Amb. Muhammad Isa Umaru ya dau matakin dakile matsalar inda yayi hani da cire yara a matakin farko wato firamari.
Sarkin ya jadada cewa, dole a bar yara mata su kammala firamari kafin a aurar da su a fadin kasar masarautar.
Kamar yadda magatakardar masarautar Nasiru Habu Faragai ya bayyana a zantawarsa da Jaridar AiRerporters, ya ce sarkin yayi wannan kalaman ne a taron da hukumar SUBEB ta shirya hadin gwiwa da UNICEF don maida yara makarant na zangongon shekarar 2025 zuwa 2026 a garin Lausu.
A cewarsa, sarkin ya gargadi hakimar, dagatar, masu unguwanni, sarakunan Fulani da malaman addini kan su tabbatar ba’a karya wanan dokar ba.
Daga karshe yayi kira ga iyaye da su baiwa yayansu dama wajen samun ilimi mai inganci, wanda ya bayyana ta hakanne yayansu zasu samu ilimi mai inganci.
KU BIYO MU A FACEBOOK