Daga Abdullahi Alhassan.
Wani Mallamin Addini Musulunci dake Kaduna kuma Shugaban Kungiyar Marayu dake Abakwa a Kaduna ,Mai suna Abakwa Orphanage Foundation.
Malam Abubakar lmam. Yayi Kira ga Gwamnatin Tarayya dana Jahohi da kananan hukumomi da suyi wani tsari na tallafawa Kungiyoyin Marayu a tsarikansu yayin Kasafin Kudi don ragewa lyayensu Marayu halin dasuke shiga bayan Mutuwa Mazajensu.
Mallam Abubakar Iman ya koka da halin da Marayu ke ciki a Najeriya na rashin kayayyakin more Rayuwa Musamman ma Abinci da daukar nauyin Karatun su a halin yanzu.
Inda ya yi kira ga masu hannu da Shuni da ma dai dai kun Mutane da su tai makesu, dan rage musu matsanancin halin da suke ciki kamar yarda hakan keda lada mutuka a Addini Musulunci.
Malamin addinin Musuluncin ya baiyana haka ne yayin da Kungiyar tallafawa Marayun dake Abakwa a Karamar hukumar Kaduna ta arewa ke raba kayan Sallah dana abinci ga lyayen Marayun don gudanar da Sallah cikin yanayi Mai Kyau .
Ya kara da cewa baya ga rabon kayan abinci lokacin Azumi da Sallah Kungiyar aiyukanta basu tsaya nan kawai ba sun hada da koyar da Marayun Sana’oi daukar nauyin karatun wasu dai dai kunsu dama biyan Kudin kammala Karatun Sakadire wato NECO/WAEC, don dogaro da kansu nan gaba tunda ilmi wajibine a kowani lokaci, haka kuma munada tsari na bama lyayen Marayun tallafi na Jari don gudanar da Sana’a da zai basu halin kula da Marayun dake karkashin kulawarsu.
Daga nan sai ya karata ayoyin Alkur’ani mai girma dama hadisai dake nuna dubin lada dake cikin ciyarwa dama tallafawa mabukata koda ba lokacin azumi ba da Sallah.
Shi kuwa Babban Limamin Masallacin Abakwa Mallam Umar Abubakar, nuna mutukar godiyar sa yayi kan wan nan karamci tare kuma da kira ga masu Karfi cikin al’umma dasu taimaka wa mabukata lura da halin ake ciki na mawuyacin hali Musamman ma ga Marayu, inda yace Annabi S.W.A.yace lna tare da wanda ya taimaki maraya a Aljannah.
Ya kuma cigaba da cewa irin wan nan aikin zaisa Marayun suji lalle al’umma batayi watsi da suba , wan nan nauyi ne na al’umma don ba musan gawar fari ba , kila kaima ko nima in Mutu kaga yayanka sun zama Marayun kenan to kaga ya zama nauyi ne a kan kowa kenan,
Daga karshe ya yabawa wadan da suke cigaba da tallafawa wan nan kungiyar tare da yi musu addu’ar samun gidan Aljannah.
Iyayen Marayun nuna Mutukar godiyar su sukayi da wan nan karamci inda suka ce zasuyi Sallah kamar kowa sun yabawa dai dai kun Mutane da suka tallafa wa wan nan Kungiyar.