Rundunar ‘yan andan Najeriya ta kaddamar da gidan rediyo na kanta da zummar inganta dangantakar da ke tsakaninta da jama’a.
Babban sufeton rundunar ‘yan sandan Mohammed, wanda ya kaddamar da gidan rediyon mai suna Nigeria Police 99.1FM Radio ranar Laraba a Abuja, ya ce gidan rediyon zai taimaka wajen rage aikata laifuka ta hanyar watsa labarai game da yadda za a kama masu laifuka da ma hana aikata wasu laifukan.
“Tuni gidan rediyon The Nigeria Police 99.1FM ya soma gudanar da aiki na gwaji kamar yadda dokar hukumar kula da kafafen watsa labarai ta tanazar. Gidan rediyon zai zama wata hanya da rundunar ‘yan sandan Najeriya za ta tattauna da wayar da kai da kuma ilimantar da ‘yan kasar game da ayyukanta da kuma sauran lamuran da suka shafi harkokin tsaro,” in ji Mohammed Adamu.
Ya kara da cewa gidan rediyon zai rika gabatar da shiri na kai-tsaye da ‘yan kasar za su rika kiran waya game da yanayin tsari a yankunasu musamman kan yadda za su gano masu aikata laifuka da bayar da rahoto a kansu ta yadda jami’an tsaro za su yi saurin kai musu dauki.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER