Sabon rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ibadan, jihar Oyo, yayinda hukumar yan sandan jihar Oyo ta bayyana cewa ta kwantar da kura a unguwar.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi, ya bayyanawa BBC cewa babu wani tashin hankali saboda ta kwantar da kuran yanzu.
Fadeyi wanda yace ba’a rashin rayuka ba, ya bayyana cewa shugaban yan sandan yankin ya tura jami’ai da wuri.
Amma a hirar da BBC tayi da al’ummar Hausawan yankin, sun bayyana cewa hankalinsu ya tashi da yammacin jiya.
Wasu mutane da suka gudu daga muhallansu sun samu mafaka an unguwar Sabo kuma bayyana yadda rikicin ya barke.
Daya daga cikinsu yace, “Yayinda nike bacci kafin Sallar Asuba, na ji mutane suna gudu kan babura. Sai aka fad amin rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa. Ina jin harbe-harbe.” ”
Wani Bahaushe dan babur ne ya buge wata mata Bayarabiya, sai yan uwanta suka damkeshi kuma suka lallasa shi. Haka ya sa Hausawa suka shiga kare nasu. Yanzu haka ina mafaka a Sabo.
An harbi mutum uku amma ba’a sani ko sun mutu ba.” Unguwar Apata wata unguwace da Hausawa masu sayar da kayan miya ke zama a Ibadan.