Da farko kamar bazanyi rubutu game da wannan abin da ya daɗe yana cimin tuwo a ƙwarya ba, dalili kuwa shine, waɗanda zanyi dansu ba karantawa zasuyi ba kuma ba lallai saƙon ya isa garesu ba saboda mafi yawancinsu basu ma san ina suka sa gaba ba.
A ƴan shekaru huɗu da Allah yabani damar zuwa wasu garuruwa na kudancin Najeriya, na haɗu da mutanenmu matuƙa, hasali ma duk inda naje mutanenmu nake fara neman inda zan samu, dan inji labarin gari da kuma yadda rayuwa take a garin.
Babban abinda yafi bani takaici ya ɓata min rai shine, yawancinsu sana’oi suke na ƙasƙanci wanda kuma idan mutum na da lafiyar lissafi yasan ba wani abu da wadannan harkokin zasu tsinanawa mutum a irin wannan rayuwar da muke ciki. Yadda Allah ya albarkaci wannan yanki na Arewacin Najeriya da abubuwa na sana’a masu tarin yawa sai ka rasa hau ne ko rashin hankali ne ke kai wasu zuwa kudancin Najeriya dan nema.
Ko da cewa yawancinsu mutanen ƙauye ne, amma na fahimci rashin wayar da kai da kuma mahimmanta kai shine asalin abinda ke kaisu irin wannan guraren. Daga masu babur, sai masu yankan farce, sai masu amalanke, sai kuma masu aiki na dako. Ba sana’oin bane damuwata, shin sun rasa wajen irin wannan sana’oin ne a Arewa?
Irin wulaƙanci da rainim hankali da ake musu shine yafi sosa min rai.. Mutannennan suna da Iyaye, wasu na da Iyalai, amma sai karasa wani lissafi ne zai sa mutum yabaro cikin yan’uwansa da suke a watse cikin Jahohi sha tara na Arewacin Najeriya.
Na fahimci wani abu ɗaya a hirar da nayi da mutane mabanbanta, yawancinsu abinda ke musu daɗi da zaman irin wadannan garuruwan zallar son bariki ce da kuma tsantsar ƴanci ba mai hanaka ba mai sa ka.
Inda zuwa ne dan kai wata Haja, ko yin wata sana’a mahimmiya wannan lamarine na sambarka, amma yadda ake kwasarsu a jibga su a motar Shanu su tafi a wulakance haka yawancinsu ke dawowa.
Lallai yana da matuƙar mahimmanci duk inda muka haɗu da masu irin wannan baragubin tunanin mu dinga wayar musu da kai, kuma mu nunar musu illa da rashin makoma mai kyau dake tattare da haka.