Rubutun: Ibrahim Musa
Akwai wrong assumptions da yawa na rashin sanin yaya aikin asibiti ke wakana. Na fahimci hakan a dambarwar dake faruwa tsakanin AKTH da Berekete Family. Gaba daya masu shirin Berekete sun tafi ne a matsayin CS akai aka cirewa matarnan mahaifa bada iznininta ba.
Farko dai nakuda ta kan rikice ta zama lalurar dake bukatar aikin gaggawa (emergency), kamar a yanayin jijjiga (eclampsia), kecewar jini (antepartum hemorrhage), fashewar mahaifa (ruptured uterus), dss. Idan mace tana nakuda sai mahaifarta ta fashe, to ta shiga yanayin emergency da ceton ranta shine mafi a’ala. Jinin jikinta zai iya karewa cikin yan dakikoki kadan. A wannan yanayin likita yana da damar cike emergency form domin samun iznin ceto rayuwarta ba tare da anbiya kudi ba. Idan an ceci rayuwar matar, wani lokacin harda da dan ko yar, daga baya sai danginta su biya kudin aikin. Duk wani abu da zai kawo delay ana kawar da shi domin a fifita ceton ranta.
A cikin tiyata, likita zai yi yanka mai fadi (laparotomy) saboda gaggawa da ake bukata kada jinin jikinta ya kare ta rasu. Sannan idan ya tarar da mahaifar zai duba yaga fashewar kadance da za a iya gyarawa ko kuma tayi kacakaca da sai dai a cire (hysterectomy) domin a ceci ranta? Wannan duk abubuwa ne da sai a cikin dakin tiyata za a gani ba a waje ba.
Ina House Officer a O&G department na AKTH, wata mata ta taba zuwa na dubata na ga dan dake cikinta ya mutu (IUFD). Daga taje tayi scanning da ta dawo har jini ya kece mata. Wallahi har mun shiga tiyatar wata mata mai eclampsia, an fara bata anesthesia sai wata likita ta keto tiyata da gudu tace idan bamu fara yankawaba mu sauketa ga wata tana zubar da jini kamar famfo. Haka na cire rigata ta tiyata na falfala da gudu zuwa blood bank na karbo robar jini shida na dawo muka ceci ran matarnan. Kun san wani abu? Tazo asibitin bada dan rakiya ba, bamu san kowa nata ba. Sai bayan an ceci ranta, ta farfado da kwana biyu, ta gaya mana sunan mahaifiyarta muka je muka taho da ita. Operation din da mukai na ceton ranta babu consent, babu wanda ya biya kudi, babu komai- ranta kawai duk yafi wadannan abubuwa muhimmanci. Amma danginta da suka zo sun biya duk ananda aka kashe, kuma sukaje suka bada robar jini shidan da na aro mata a blood bank.
Wannan matar da ake ta zagin AKTH akanta, da a lokacin da mahaifarta ta fashe, likitoci sunyi burus da ita sunce sai an biya kudi kafin su shiga tiyatar emergency, da yanzu wani zancen ake daban. Da yanzu ana maganar yau shekara sha biyar kenan da rasuwar wance.
Aikin likita akwai hadari sosai. Muna House Officers, sama da awa 48 muke muna yin weekend call- tun ranar Asabar sai Litinin mun gama ward round da rana zamu koma gida. Akwai takaici ka gama bada rayuwarka domin ceto ran mutum amma rashin sani yasa ya mayar da abin ya zama kamar cutar da shi kayi. Su kuma yan amshin shata suyi ta zagin wadanda basu aikata laifin komai ba sai ma alheri da sukai na ceton rai.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA X