Daga – Abdullahi Alhassan Kaduna
Kwararru a fanin aikin Jarida sun koka Kan yanda ake cigaba da daukan masu Kiran kafafen yada labarai dama Wanda basu kwareba amatsayin yan Jarida a wasu kafafen yada labarai a matsayin ma’akatan aikin Jaridan,
Kiranya fito ne daga bakin mataimakin Darakta Sashin Afrika na Wakilan masu rahotonni Kan abinda ya shafi dumamar yanayi,wato (African Climate Reporters)
Dakta Piman Hoffman,yace bai dace ba Kamar yarda wasu kafafen yada labarai ke cigaba da daukan masu Kiran waya dama wanda basu kwarw ba a kafafen yada labaran amatsayin yan Jarida ko ama’aikantan kafafen yada labarai don kare martabar aikin Jaridar,
Ya Kara dacewa a akwai bukatar kare aikin Jaridan ganin yarda ake cigaba da masun wadan da basu kwareba ba da suke cigaba da kwarara a cikin aikin Jaridar, ganin cewa suna cigabada kawo wa aikin cibaya a fagen aikin Jaridar.
Ya Kuma cigaba da cewa a kwai bukatar kare Kungiyar yan Jarida ta Najeriya N.U.J da Kungiyar kare aikin Jaridan wato National Press Council, dama Hukumar da ke kula da Kafafen yada labarai,da Kuma Sauran Kanfanonin dillancin labarai,sun himmatu wajen hada hannu don magance matsalar da ke cigaba da kawo cibaya ga aikin Jarida a Najeriyar.
“Akwai bukatar hada gwiwa don ganin an kawo karshen matsalar daukan wanda baso kware ba da ma bara gurbi a matsayin yan Jaridar,
Mataimakin Darakta ya dora laifin ga Kafafen yada labarai masu zaman kansu da daukan wanda basu kwareba amatsayin yan Jaridan wanda basu san dokoki da ka’idojin aikin ba,
Ya Kara da cewa irin wan nan Kafafen yada labarai suna daukan wadan nan irin wanda basu kwareba ba ne don ganin cewa su basu San Kan aikin ba da Kuma ba wani abin kirki suke basu ba amatsayin hakkin su ko Albashi ba, “duk da cewa a kwai wadan da suke karanta aikin Jaridar daga inda ake Koyar da Kwararru dake da takardun shaidar aikin Jaridar da sukafito daga Jami’oi da ma Kwalejojin Kimiya da Fasaha inda ake horar da Kwararru don sanin aikin.
Shi kuwa wani Kwarenren dan Jarida daga Cibiyar yan Jaridan masu rahotonni Kan abinda ya shafi dumamar yanayin, Muhammad Ibrahim,yace ya yi wan nan lokaci da ake gudabar da ranar yancin yan Jaridan, akwai bukatar Kafafen yada labarai da suriga daukar Kwararru a matsayin ma’aikata don samu saukin yayin gudanar da aikin da Kuma bin dokuki da ka’idojin aikin Jaridar ba tare da samun wasu matsaloli ba lokacin gudanar da aikin nasu ba,
Kwarenren ya Kara da cewa “lna Kira da Kafafen yada labarai da su kula da hakkin ma’aikatan na ganin su basu Albashin su kan Kari don karfa fa musu kaimi gudanr da aikin nasu,
Haka kuma su Samar musu da kayan aiki na Zamani don tunkarar aikin bare da samun matsala ba tare Kuma da horar da su kan rahotonni da zasu kawo cigaba cikin Al’umma.
Ya yi Kuma Kira ga yan Jaridun Duniya da Su kaucewa gubataccen aikin Jaridar da zai kawo tashin ta shina a kasa inda yace a hada gwiwa da Gwamnatin Tarayya da Jahohi dama masu da ruwa da tsaki kan yada labaran da zasu kawo zaman lafiya don yaki da yada labaran bugi dake cigaba da yawo kafar sada zumunta,
Cibiyar tayi Kuma Kira ga Kungiyar yan Jaridan ta kasa da ta tabbata Kafafen yada labarai na biyan Ma’aikatan nasu Kan kari don kaucewa shiga hakkinsu,
Daga karshe Cibiyar tace ganin yarda ake cigaba da samun Karin yaduwar Annobar Corona Virus akwai bukatar horar da yan Jaridan Kan ilmin Kimiya don tunkarar kalubalen cigaban yaduwar Chautar a Duniya.
Shi kuwa wani Mai rike da Sarautar Sardaunan Unguwar Sarki Musulmi dake Kaduna,Alhaji Abdulkarn Musa ,Kira ya yi da Gwamnatin Tarayya da Jahohi da su himmatu wajen karfafa wa yan Jaridan da basu kulawa ta Musamman,lura da rawa da suke da lta cikin Al’umma, ganin cewa suna cigaba da wayar ilmantar da Kan Jama’a ta hanyar Samar dasu Kan halin da Duniya keci , kamar yarda suke zama Dilka da Hudu dake rike da Tirakun tsayuwar Mulkin Dimukuradiya a kasa tare Kuma da Kyautata Albashin su da Sauran hakkokin su,
A karshe ya yi Kira da Majalissar kasa da suyi doka da zata cigaba da kare Rayukan su da don ganin sun sauke nauyin da Kundin tsarin kasa ya dora musu.