ABDULLAHI ALHASSAN KADUNA.
Shugaban Kungiyar yan uwa Musulmi Mabiya Mashabar Shi’a dake Kaduna ,Shiekh Ibrahim Yakub Alzakzaky ya raba kayan abinci da kudi don kammala Azumin watan Ramadana da gudanar da Sallah cikin yanayin walwala ga Musulmi da ma Mabiya addinin Kirista don rage musu matsanancin halin da ake ciki,
Kayan abinci da suka hada da Shinkafa Gero da Kudi wanda akalla ko wani Mutum ya samu daga 15,000 Zuwa dubu 30,000
A Cikin wadan da suka anfana dawan nan tallafin na Sheikh Zakzakin sun hada da Yan Jarida, da Masu aikin cigaban Al’umma, da Maza da Mata Yan kasuwa da Kiristoci da Musulmi ,
Wani da ya amfana da tallafin kayan abinci dama Kudi yace,”Mr. Ezekiel Bavorang dake zaune a Nasarawan Kakuri daga Karamar hukumar Kaduna ta Kudu, godewa Malamin ya yi na samusu wan nan farin cikin ganin cewa za suyi anfani da shi a abukukuwa,
Ya kuma kara godewa Malamin Kan buhun Shinkafar da ya samu da Kudi har naira dubu 3 wan nan zanyi anfani da lta har tsawon kwata Talatin masu zuwa nan gaba kasan cewa abincin da yawa gaskiya,
Bavorang ya Kara da cewa amatsayina da Kirista shi Kuma Musulmi Kuma Shugaba wan nan ya nuna yarda yake Kira don nuna kaunar Juna kasan cewar mu daga Addini dabam,
Ita kuwa wata yar kasuwa Ladidi Shehu wacce ta samu Kudi har naira dubu 3 da Kuma rabin buhun shinkafa da Gero da ke gudanar da karamar Sana’a a kasuwar Shiekh Abubakar Gumi a Kaduna,cewa tayi wan nan zai rage mun halin dake ciki gaskiya na mawuyacin halin da ake ciki,lura da cewa ni Mijina ya mutu Kuma ya barmun Yara kanana a gabana, lna Kira da Sauran Mawadata da suyi koyi da irin jinkai na wan nan Malami na tausayawa Jama’ a na wan nan mawuyacin hali.
Daga karshe tayi Kira da Allah ya saka masa da mafi Alheri sa.