WATA KUNGIYA TA MATASA MAI ZAMAN KANTA MAI SUNA ‘NIGERIAN YOUTH LEADERSHIP INITIATIVE’ TAYI TARON GANGAMI A KATSINA, NA WAYAR DA KAN MATASA DA KUMA KIRA GA SEN. GODSWILL AKPABIO DA YA FITO TAKARAR SHUGABANCIN KASAR NAN A SHEKARA TA 2023, A BISA WASU AYYUKAN CI GABA DA YAYI MA KASATA NIGERIA (FORENSIC AUDIT NDDC).
A Jiya juma’a 10 ga watan tara 2021, misalin karfe goma na safe a babban dakin taro na 3As da ke rukunin gidajen Fatima Shema akan titin ring road Katsina, kungiyar mai suna ‘NIGERIAN YOUTH LEADERSHIP INITIATIVE’, ta gabatar da taron domin kira ga MATASA da su zama masu ruwa da tsaki a cikin harkokin siyasa da shugabanci a fadin kasar nan, taron ya samu halartar kungiyoyin matasa daban daban a fadin jihar nan ta Katsina.
A yayin Dr. Aliyu Umar Abubakar Funtua ya shugabanci taron, sai kuma urban taro Sarkin Aikin Kasar Hausa na 1, Engr. Kabir Ya’u Yamel, sai Wanda ya shirya taron Comrade Emmanuel Amama daga jihar Akwa Ibom sai kuma shugaban Kungiyar ‘MATASA INA MAFITA’ reshen jihar Katsina Comrade Usman Rabi’u Mahuta shima ya gabatar da kasidarsa akan matasa su shiga harkar siyasa gadan gadan a fadin kasar nan.
Taron ya hada da Comrade Al’amin Rabi’u Mani Wanda tsohon (S.A ) kuma ya yabi Sen. Godswill Akpabio akan irin ayyukan da yayi na jihar shi Akwa Ibom, ya Kara da cewa Sanata Godswill mutum ne na musamman Wanda samun irinshi a shugabanci zai kawo ci gaba ga matasa da Al’umma gaba daya a kasar nan.
A cikin jawabinsa Sarkin aikin kasar Hausa na 1, ya fara da sama kungiyar albarka kuma yace zai tsaya ma kungiyar akan wannan kira da ta ke ma Sanata Godswill Akpabio a inda ya kamanta shi da cewa mutun ne mai cika alkawari akan abinda yace zai yi.
Kungiyoyin sunyi la’akari da irin namijin kokarin da Sanata Akpabio yayi a karkashin Ministry din da ya ke jagoranta, ta Niger Delta (NDDC), Wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dora ma alhakin kula da ita, a yayin da yayi nasarar bankado almun dahana da aika aika a babbar hukumar NDDC, ya kuma yi nasarar Gina ma hukumar mazauninta na dindin a Portharcourt Wanda shekaru ashiri da hudu da suka wuce tana zaune a gidan haya, ya kuma yi nasarar gyara babban filing saukar jiragen sama na kasa da kasa (Victor Attach) a Akwa Ibom State, sai kuma ya gina katafaren filin wasanni mai suna Godswill Akpabio international stadium a Akwa Ibom sannan ya tilasta harkar Ilimin Primary da Sakandire kyauta a jihar shi.
A bangaren arewa kuma wani ma’aikacin jami’ar Alqalam University ta Katsina Sani Bature Saulawa ya fadi cewa Sanata Godswill Akpabio ya bada lambar yabo ga wasu kwararrun dalibai da kudi dake makarantar Hussaini Adamu Polytechnic Kazaure Jigawa State.
Sai kuma a 2010 shugaban makarantar Hussain Adamu Polytechnic ya gayyato Sanata Godswill Akpabio a inda gina masu katafaren hostel a cikin makarantar Wanda a yanzun haka suna anfani da shi.
Sai kuma jami’in hudda da jama’a na kungiyar Alhaji Mukhtar Sani (Bindawa), Wanda ya gabatar da kudirorin kungiyar ya kuma yi kira
ga matasa da su bada gudun mawa da goyon baya a bisa kan kudirorinshi na alkhairi.
Sai chairman din taron ya bayyana Senata Godswill Akpabio a matsayin mutumin kirki kuma yace kungiyoyin da dama wadanda suka bayyana Kansu da ma wadanda basu bayyana Kansu ba cewa ya zama cikin shiri domin shine Wanda zasu tsaida a matsayin Dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023, Dr. Aliyu ya kara da cewa yanzun haka kungiyoyin sunci gaba da shirye shiryensu na mara ma Senata Godswill Akpabio a matsayin dan karar shugaban kasa insha Allah, ya kuma kara da cewa wannan kungiyar yana ci gaba da had a kawunan kungiyoyi a kalla matasa million Hamsun a fadin kasar nan zasu hada matasan arewa da matasan kudu Inda zasu Samar da matsaya daya domin ci Gaban al’umma.
By
Comrade Usman Rabu’u Mahuta
Director E- Media
Nigerian Youth Leadership Initiative