Hukumar hana sha da fatauncin miyagun kwayoyi NDLEA ta Najeriya ta ce ta kama wani mutum dan shekara 70 da ake zargi dai kai wa ‘yan bindiga kwaya.
Cikin wata sanarwa da ta wallafa a Twitter, hukumar ta ce, mutumin mai suna Muhammad Rabi’u Wada da ke kai wa Boko Haram da ‘yan bindiga kwaya an kama shi ne a jihar Neja.
NDLEA ta ce mutumin na zuwa ne daga jihar Agadez ta Jamhuriyar Nijar ne, ya shigo da kayan Najeriya.
A wani aikin da hukumar ta yi mai kama da wannan, ta samu nasarar lalata gonar taba a jihar Ondo da ke kudancin Najeriya wadda girmanta ya kai hekta 95.
An samu gonar ne a dajin Ogbese, sai dai ba a samu nasarar kama kowa ba yayin samamen, amma ana ci gaba da bincike domin gano mai gonar.
A jihar Kogi da ke arewacin kasar Hukumar ta samu nasarar kwace tabar da ta kai kilogiram 116.1 wani shingen ababan hawa a yankin Okene-Lokoja.
Mutumin da aka kama da kayan mai suna Sulaiman Said ya ce ya ɗakko kayan ne daga jihar Edo kuma zai kai su Jihar Kaduna ne.