Mataimakin shugaban jam’iyyar Apc na shiyyar Funtua ya yi taro da shugabannin mazabun shiyya (117) na Apc.
A ranar Juma’a 03/09/2021 ofishin Mataimakin shugaban jam’iyyar Apc mai kula da shiyyar Funtua karkashin jagorancin Alh. Bala Abubakar Musawa ya kira taron sada zumunci da zababbun shugabannin jam’iyyar Apc na mazabun shiyyar Funtua (117).
Manufar taron domin a gana dasu a san juna, domin mafi akasarinsu sababbi ne, yayin taron Alh. Bala Abubakar Musawa ya bayyana” ma sababbin shugabannin jam’iyyar mazabun yadda jam’iyyar Apc take a shiyyar Funtua dunkule tsintsiya Madaurinki daya, ya cigaba da cewa” haka kuma muke bukatar ta cigaba da tafiya domin kaucema samun duk wata baraka da zata kawo rarrabuwar kai cikin jam’iyyar a shiyyar Funtua.
Daga karshe Alh. Bala Abubakar Musawa ya yi kira” ga shugabannin jam’iyyar da suci gaba da addu’a akan jarabawar da Gwamnatin Apc ta samu kanta a ciki na matsalolin tsaro da suka addabi kasar nan, wanda abun ya shafi Jiharmu ta Katsina.
Shima a nashi jawabin Alh. Shamsu Sule Funtua (Dugaji) jawo hankalin shugabannin jam’iyyar ya yi” akan dasu guji daukar dukkan wani Dan takara, sanin kowa ne jam’iyyar Apc a shiyyar Funtua abu daya take tafiya akanshi watau umurnin Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari CFR.
A nashi jawabin mataimakin Kakakin majalisar Dokoki ta Jihar Katsina kuma Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Faskari Hon. Shehu Dalhatu Tafoki ya jaddada ma shugabannin jam’iyyar mahimmanci hadin kai, domin saida hadin kai ake samun nasarar tafiya kowace irice.
Taron da aka gudanar a Unguwar Sardauna Estate dake cikin garin Katsina, ya samu halartar wasu daga cikin yan majalisar Jiha da suka fito daga yankin na Funtua, cikinsu harda Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina Hon. Shehu Dalhatu Tafoki, sai Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Danja Hon. Shamsuddeen Abubakar Dabai Chiroma.
Sauran sun hada da, Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Sabuwa Hon. Ibrahim Danjuma Machika, Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Malumfashi Hon. Aminu Ibrahim Malumfashi, Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Musawa Hon. Lawal H. Yaro Away.
- Tsoffin kantomomin rikon kananan hukumomi daga suka fito daga shiyyar, da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar Apc na shiyyar Funtua. Dadai sauransu.
Share this…