Rahotanni daga birnin Sokoto fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ,Dr Sa’adu Abubakar lll na bayyana cewar Sarkin Musulmin ya yi zargin cewar wasu fitattun mutane ‘yan kasar da suke da yakinin cewar za su iya juya ta yadda suke so na kokarin ganin darewarta domin biyan bukatun kansu na son zuciya.
Sa’adu Abubakar ya bukaci hukumomin kasar da su tashi tsaye wajen ganin dawo da martabar Najeriya saboda abin da ya kira illar wadannan mutane da ba sa bukatar kasar da alheri, aniyarsu ta koma a kansu.
Sarkin Musulmin ya ce wadannan mutane na taka rawa sosai wajen ganin Najeriya ta rabe, saboda haka suna da nauyin da ya rataya a kansu na tashi tsaye domin kalubalantar su, kuma a dage wajen ganin mummunar haƙarsu ba ta cimma ruwa ba.
Shugaban Majalisar Sarakunan Najeriya ya ce, yana da muhimmanci talakawa su fahimci cewar suna da rawar da za su taka saboda nauyin da ya rataya a kansu, domin babu wanda ya isa ya sa su su yi abin da bai dace ba, bisa ga haka ya kamata kowa ya hankalta.
Mai alfarma Sarkin Musulmin ya ƙara da cewar wannan ya sa shugaban kungiyar Izala Sheikh Sani Yahya Jingir ke cewa da kuri’unku kuna iya sauya gwamnati cikin kwanciyar hankali amma ba da tashin hankali ko satar kuri’u ba.
Sarkin Musulmin ya ce lokaci ya yi da jama’a za su sake tsarin tafiyarsu domin samun shugabanci na gari, wanda zai wanzar da adalci da kuma tabbatar da amana domin kuwa kowa zai bada ba’asin rawar da ya taka gobe kiyama.
Mai Alfarman ya tunatar da shugabannin fahimtar matsayin addu’ar ‘yan Najeriya da aka zalunta wanda hakan kan iya haifar da koma-baya ga yadda kasar ke tafiya, yayin da ya yi kiran ci gaba da zaman lafiya.