Manoma a Jihar Neja suna kokawa kan yadda farashin kayan abinci, musamman hatsi, ke ta sauka ba tare da tsayawa ba. Sun danganta hakan da matsalar kamfanonin Najeriya da suka koma sayen kaya daga ƙasashen ƙetare.
Manoman da ’yan kasuwa sun bayyana cewa wannan faɗuwar farashi na barazana ga rayuwarsu, duk da cewa ’yan Najeriya sun yi maraba da rahusa da ake samu a farashin abinci.
Hassan Ango Abdullahi, Shugaban Ƙungiyar Manoma ta Amana Farmers and Grains Suppliers of Nigeria, reshen Shiroro, ya tabbatar wa wakilin Aminiya cewa farashin kayan abinci ya sauka sosai a wasu manyan kasuwannin jihar.
Ya ce kamfanoni yanzu sun fi sayen kaya daga ƙasashen Chadi, Ghana, da wasu ƙasashe saboda farashin can ya fi sauƙi. Abdullahi ya bayyana cewa a farkon lokacin rani, buhun wake mai nauyin kilogiram 100 ya kai N103,000, yayin da waken soya ya kai N105,000. Sai dai yanzu farashin ya sauka zuwa N80,000.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA X