Masarautar Saudiyya ta sanar da cewa mahajjata 60,000 ne za a bai wa izinin shiga aikin hajjin bana na shekarar 2021.
Ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta ce, adadin zai hada da mahajjata na gida da na kasashen waje.
Sanarwar ta biyo bayan rashin tabbas idan aikin hajjin na 2021 zai gudana bayan masarautar ta dakatar da aikin hajjin 2020 saboda annobar Korona.
An rage adadin mahajjata bisa ka’idoji annobar kamar yadda kasar ta saba karbar baklkuncin musulmai miliyan biyu masu aminci zuwa garin Makka mai alfarma.
A cewar sanarwar, “mahajjata dubu 60 ne za a bari su yi aikin Hajjin bana wanda ya hada da mahajjata na gida da na waje.”
“Wadanda zasu yi aikin Hajjin dole ne su kasance tsakanin shekarun 18 zuwa 60. Wadanda ke aikin Hajjin dole ne su kasance cikin koshin lafiya sosai,” in ji ta.
“Wadanda zasu yi aikin hajjin sai an tabbatar cews ba su kasance a asibiti ba saboda wata cuta a cikin watanni 6 da suka gabata kafin tafiya aikin Hajjin, wanda hakan ya bukatar hujja. Dole ne mahajjatan ya kasance sun yi allurar riga-kafin duka tare da katin riga-kafin da kasashe daban-daban na kiwon lafiya, Asibiti ko ma’aikata suka bayar, shi ma ana bukatar hujja,” in ji ta.
Zuwa rubuta wannan labarin dai ba mu samu alkaluman da aka ware wa Nijeriya cikin adadin masu tafiya ba.