Daga: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
A yau matsalar barayin waya ta zama ruwan dare a cikin al’umma. A kowanne lokaci sai an samu rahoton cewa an sace waya daga hannun mutum, wasu lokuta har da kisa ko mummunan lahani da amfani da muggan makamai.
Wannan matsala na ƙara yaduwa musamman a cikin manyan birane ,unguwanni,tituna kuma duk masu aikata haka duk an sansu da gidajen su da iyayen su.
1. Fahimtar Illar Satar Waya: Wayar salula ba kawai ta kiran waya ba ce, tana dauke da muhimman bayanai kamar hotuna, sakonni, bayanan banki da lambobin sirri. Idan barayi suka sace waya, za su iya amfani da ita wajen cutar da mai ita ko wasu. Don haka, fahimtar girman wannan matsala shi ne mataki na farko.
2. Kafa kwamiti mai karfi na matasa masu kishi da tarbiyya da dattijai da jamian tsaro, domin ɗaukan mataki da saka ido, da tabbatar da doka da oda,domin kar tasan kar.
3. Ya zama dole gwamnati ta tsananta hukunci ga masu aikata laifin satar waya. Dole ne a horar da jami’an tsaro su dauki satar waya da muhimmanci kamar yadda ake daukar sauran manyan laifuka. Haka kuma, kotuna su rika hukunta barayin waya bisa doka.
3. Amfani da Lambar IMEI: Kowace waya tana da lambar IMEI (International Mobile Equipment Identity) da za a iya amfani da ita wajen gano inda take ko hana amfani da ita. Idan an sace waya, za a iya kai rahoto ga ‘yan sanda da kamfanin sadarwa domin su kulle wayar. Ana iya ganin lambar IMEI ta hanyar kira *#06# a wayarka.
4. Wayar da Kai da Ilmantar da Jama’a: A shirya tarurruka da shirye-shiryen rediyo da talabijin don fadakar da jama’a game da satar waya da yadda za su kare kansu. A koya musu su daina siyan kayayyakin da ba a san asalinsu ba, musamman wayoyin da ake zargin an sace.
5. Ya kamata mutane su sanya kariya ga wayoyinsu ta hanyar amfani da password, PIN, fingerprint ko face ID. Haka kuma, a girka manhajoji kamar Find My iPhone ko Find My Device domin iya gano inda wayar take idan aka sace ta.
6. Kada mutum ya yi amfani da waya a waje, musamman a wuraren da ake cunkoso. Kada a bar waya a fili , a saka waya a cikin aljihu ko jaka mai kyau.
7. A wayar da kai game da daina siyan kayayyakin sata.
8. Ayyana ɓarayin waya da suke Amfani da makami a matsayin ƴan fashi da makami ,da hukunta masu goya musu baya na Iyaye ko Yan siyasa da Masu siyan kayan da suka sato da matsayin dukkan su masu laifi ne iri ɗaya.
9. Ware wata kotu ta musamman domin yin hukunci ga masu aikata haka da zartar da hukunci cikin gajeren lokaci da Kuma aiwatarwa.
10. A haɗa da yaƙar masu siyar da ƙwaya ta hanyar aro hukuncin da Saudiyya suke dauka na fille Kan masu shiga da ƙwayoyi ƙasar.
Idan kuna da ƙarin shawarwari ku faɗa domin mu miƙawa mahukunta.
Allah ya shiryi matasan mu.
KU BIYO MU A FACEBOOK