Daga Abdullahi Alhassan.
Sanata mai wakiltar mazabar Katsina ta Tsakiya a Majalissar Dattawa, wato Sanata Injiniya, Kabir Abdullahi Barkiya , yace sun karbi kudirori da bam da bam a zaman da sukayi na kwana biyu a Shiyar Arewa maso yamma da ya gudana a jahar kaduna.
Sanata Barkiya yace Kudirorin da suka karba sun hada da Kirkiro Jahohi da ga Jahohin dake wan nan Shiya kamar a Kaduna Kirkiro Jaha Gurara wanda Al’ummar Kudanci Kaduna suka gabatar wato Sokapu, da kuma neman Karaduwa daga Jahar Katsina sauran sun hada da Kano inda Suka nema a kirkiro Jahar Ghari da Tuga , sai kuma wanda ya nemi a Chanza wa Karamar hukumar Kunci dake jahar zuwa Ghari, haka ma an samu ra’ayi don kirkiro jahar Hadeja daga jahar Jigawa a yau.
Ya kuma cigaba da cewa sauran bukatun sun hada da kirkiro Yan sandan Jahohi don Taimakawa matsalar tsaro, Su kuwa Ma’aikatan Kananan hukumomi neman yancin Chin gashin Kai sukayi tare kuma da raba su daga Asusun hadaka da ga Johohi, Sanata Barkiya ya cigaba da cewa ashirye suke don ganin sunyi dokoki da suka dace da Yan Najeriya lura da cewa suna Wakiltar Kasa ne don haka daga lukaci zuwa lokaci zasu cigaba da Kwaskwarimar kundin tsarin Mulkin don samar da dokoki da suka dace da Kasar nan, Wan nan Zama dai na Karbar Ra’ayoyin Jama’a Ya gudana ne a Mazabu Shida da ake da shi a kasar nan , inda aka zauna a Cibiyoyi 12 don karbar ra’ayoyin jama’ar dake shiyar arewa maso yanma.
KU BIYOMU A FACEBOOK DA TWITTER