Kungiyar kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch ta zargi China da hannu dumu dumu wajen aikata laifuffukan cin zarafin Bil Adama akan Yan kabilar Uighur Musulmi.
Rahotan binciken bangarorin biyu yace gwamnatin China ta aikata laifin cin zarafin Bil Adama kuma tana cigaba da aikata haka akan Yan Kabilar Turkic Musulmi bayan na Uighur.
Rahotan yace China tana daukar wannan mataki ne domin share al’adun mutanen da kuma addinin su, kuma hakan ya sabawa dokar duniya da aka amince da ita a Rome a shekarar 1998.
Bangarorin biyu sun zargi China da cigaba da tsarewa da azabtarwa da kuma kashe yan kabilar Uighur da kuma azabtar da su da gangan, kana da lalata da su.