Kotun Tarayya da ke Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a S.M. Shuaibu ta yanke hukunci kan mutane 12 da aka kama da laifukan zamba ta intanet, karɓar kuɗi ta hanyar damfara da kuma wanke kuɗaɗen haram.
Wadanda aka yanke wa hukunci sun haɗa da Michael Yakubu, Udo Promise Jonah, Promise Isah Ibrahim, Samuel Odeh, Abdulsamad Muhammad, Agboeze Chibueke Ernest, Ochuba Chigozie, Abu David Eleojo, David Aaron, Chidi Destiny Chidiebere, Collins Noel, da Ola Ajibola.
Dukkanin su sun amsa laifukan da ake tuhumar su da su, inda lauyoyin EFCC suka nemi kotu ta yanke musu hukunci, yayin da lauyoyin kare su suka roƙi kotu ta yi musu sassauci.
Mai Shari’a Shuaibu ya yanke hukunci daban-daban, inda wasu suka samu hukuncin daurin shekaru 2 zuwa 5 ko kuma tara daga N300,000 zuwa N500,000. Har ila yau, kotu ta umarci a kwace wayoyi, kwamfutoci da kuɗaɗen da suka samu ta haramun, tare da mika su ga gwamnatin tarayya.
An kama waɗannan mutane ne a jihohin Nasarawa da Neja bayan samun bayanan sirri da suka bayyana yadda suke gudanar da ayyukan zamba ta kafafen sadarwa
KU BIYO MU A FACEBOOK