">
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
Wednesday, October 15, 2025
No Result
View All Result
NEWSLETTER
Daily Episode Hausa
-18 °c
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
No Result
View All Result
Daily Episode Hausa
No Result
View All Result
">

Kotu ta dakatar da yin muƙabalar Sheikh Abduljabbar da Malaman Kano

by Abubakar Ismail kankara
March 5, 2021
in Healthy Eating
0
Kotu ta dakatar da yin muƙabalar Sheikh Abduljabbar da Malaman Kano
Share on FacebookShare on Twitter
">

RelatedPosts

Hukumar Hisbah Ta Fara Kauda Yara Masu Gara-Ranba Daga Titunan Kano

Dalilin Da Yasa Ba Za Mu Murkushe ‘Yan Bindiga Ba – Buhari

">
">

Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta dakatar da yin muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da malaman Kano da aka shirya yi.

A ranar Juma’a ne Mai Shari’a Muhammad Jibrin na Kotun Majistire da ke Gidan Murtala, ya yanke hukuncin sakamakon buƙatar da wani lauya mai zaman kansa Barista Ma’aruf Yakasai ya shigar gabanta.

Barista Yakasai dai ya buƙaci a dakatar da gwamnati daga yin muƙabalar ne, saboda hakan ya ci karo da umarnin da kotun ta bayar tun da fari na hana Sheikh Abduljabbar karatu da kuma saka karatukansa a daukacin kafofin yada labaran jihar.

Sai kuma bukatarsa ta biyu da yake son ya shiga cikin waɗanda gwamnatin Kano take ƙara, sai dai ba a amince da wannan ba har sai an sanar da Abuljabbar da kwamishinan ƴan sandan jihar a cewar kotun.

Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa za ta bi wannan umarni na kotu, inda Kwamishinan Shari’a Barista Musa Lawan ya yabbatar da cewa babu muƙabala a ranar Lahadi mai zuwa.

Lauyan Barista Ma’aruf wato Barista Lukman Auwalu Abdullah ya ce sun ji dadin umarnin kotun.

Ya ƙara da cewa abin da ya sa Barista Ma’aruf ya shiga cikin lamarin shi ne saboda ya tunatar da dukkan ɓangarorin cewa bai kamata a yi muƙabala ba, duba da umarnin kotun na farko na haramta wa Abduljabbar karatu.

A ganinsa yin muƙabalar tamkar an bar shi ya yi karatun ne wanda hakan soke umarnin kotun ne da yi mata rashin biyayya.

Yanzu dai an tsayar da ranar 22 ga wata Maris din da muke ciki don sauraran roƙon Barista Ma’aruf Yakasai kan dukkan buƙatun.

DAILY EPISODE HAUSA

KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER

Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail Kankara is the founder and CEO of AIACCESS Contractors and the Managing Editor OF Daily Episode

Related Posts

Hukumar Hisbah Ta Fara Kauda Yara Masu Gara-Ranba Daga Titunan Kano

Hukumar Hisbah Ta Fara Kauda Yara Masu Gara-Ranba Daga Titunan Kano

by Abubakar Ismail kankara
December 31, 2024
0

Wanan na zuwa ne bayan da humar tasha alwashin kawo sauyi wajen gyara tarbiya da kuma kauda duk wata barazana...

Dalilin Da Yasa Ba Za Mu Murkushe ‘Yan Bindiga Ba – Buhari

Dalilin Da Yasa Ba Za Mu Murkushe ‘Yan Bindiga Ba – Buhari

by Abubakar Ismail kankara
February 27, 2021
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin tsananin fushi ya gargadi ‘yan bindiga da ke adabar al’umma a sassan kasar musanman Arewacin...

Next Post
Idan za’a gafartawa wadanda suka haddasa yakin basasa da juyin mulki me zai hana ‘yan bindiga? Sheikh Gumi

Idan za'a gafartawa wadanda suka haddasa yakin basasa da juyin mulki me zai hana 'yan bindiga? Sheikh Gumi

An kama wani soja da budurwarsa da laifin taimakawa ‘yan bindiga da kayan sojoji, da alburusai a Zamfara.

An kama wani soja da budurwarsa da laifin taimakawa ‘yan bindiga da kayan sojoji, da alburusai a Zamfara.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

">
  • Talla
  • Tuntube Mu
  • Gida
TUNTUBE MU: 08032398985 info@dailyepisode.ng

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

Login to your account below

Forgotten Password?

Fill the forms bellow to register

All fields are required. Log In

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In