Lagos, Najeriya — Babbar Kotun Tarayya da ke Ikoyi, jihar Lagos, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a D.E. Osiagor, ta yanke wa wasu ‘yan ƙasar Sin guda tara hukuncin daurin shekara guda a gidan yari, bisa laifukan da suka haɗa da damfarar intanet da ta’addanci na yanar gizo.
Wadanda aka yanke wa hukuncin su ne: Li Dong, Deng Wei Qiang, Huang Bo, Xiong Zhen, Lai Rui Feng, Zhao Xiao Hui, Lui Hai Rong, Lui Gang, da Du Ji Feng. An kama su a ranar 19 ga Disamba, 2024, a Lagos, yayin wani samame na musamman da hukumar EFCC ta kaddamar da shi mai suna “Eagle Flush Operation”. Samamen ya kama mutum 792 da ake zargi da hannu a damfarar zuba jari a harkar kudin intanet (cryptocurrency) da kuma damfarar soyayya (romance scam).
A watan Fabrairu 2025, EFCC ta gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhumar aikata ta’addanci ta yanar gizo da damfara. A da, sun musanta tuhumar, amma a zaman kotu da aka yi a ranar Alhamis, 5 ga Yuni, 2025, sun sauya matsayinsu zuwa “mai laifi”.
Bayan karɓar laifin, lauyan masu gabatar da ƙara, Nnaemeka Omewa, ya roƙi kotu da ta yanke musu hukunci. Lauyoyin da ke kare su ma sun amince da wannan buƙata.
Mai Shari’a Osiagor ya yanke hukuncin daurin shekara guda ga kowane ɗaya daga cikinsu, daga ranar 10 ga Disamba, 2024, wato ranar da aka kama su. Sannan kotu ta ci kowannensu tarar naira miliyan ɗaya (₦1,000,000).
Bayan kammala zaman gidan yari, kotu ta umarci Shugaban Hukumar Shige da Fice da ya tabbatar da cewa an maido da su ƙasarsu ta asali cikin kwana bakwai (7).
Haka kuma, kotu ta bayar da umarnin kwace duk na’urorin su kamar wayoyi, kwamfutoci, da na’urar sadarwa (routers) da aka kama da su domin a mika wa Gwamnatin Tarayya.
KU BIYO MU A FACEBOOK