Rahotan da Daily Episode Hausa ta tattara daka jaridar idon mikiya na nuna da cewa, yan bindiga dake yawan kashe mutane kana suna garkuwa dasu don amsar kudin fansa sunyi garkuwa da mutane a hanyar Abuja zawa Kaduna.
Yan ta’adar da suka tare hanyar, sunyi garkuwa da Alh Sani Ahmed Zangina, inda har zuwa yanzu lokacin da muka buga labarin, bamu samu rahotan sunyi bayyani ba.
Alh Sani dai, yayi posting a kafar sada zumunta na Facebook, inda yake bayani akan tsaro ya inganta a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Sai dai daka bisani ya gamu da iftila’in masu garkuwa da mutane, kasa da awa daya da bayanan sa kan samun ingancin tsaro.
Muna fatan Allah ya kubutar dashi, da sauran al’uma dake tsare a hannun ya ta’ada a kasar baki daya.
KU BIYO MU A FACEBOOK