Fitacchen dan gwagwarmayar nan wan da ya rikida zuwa dan takarar shugabancin karamar hukuma Kaduna ta Arewa Mallam Yusuf Idris Amoke, yace karamar hukumar Kaduna ta Arewa na da hanyoyin samun Kudin shiga da in aka yi anfani da su zai hana karamar hukumar dogara da Kudin shigar da ake samu daga Gwamnatin tarayya a kowani wata,
Honarabil Amoke ya baiyana haka ne lokacin shan ruwa bude baki ,da ‘yan Jaridu a Kaduna yace yanada tsari da zai bullo dashi ta hanyar amfani da hanyoyin da suka hada da anfani da Kungiyoyi don karban haraji a sauwake ba tare da tsare Mutane da cin zarafinsu don karban Haraji ba,hakan zai rage sulalewar harajin kamar yarda ake gani a baya,
Bugu da Kari, a matsayina na masanin muhalli zanyi amfani da matasa ta hanyar sarrafa Shara don Alkintawa zuwa abu mai amfani da zai samar wa da karamar hukumar kudin shiga,kaga kenan zakaga mata da matasa sun samu abunyi kenan zai zama duk wani rubobi ko ledoji an nema anrasa saboda an halkinta su sun zama kudi kenan,
Daga karshe yayi kira da ‘yan Jaridu akan Jaddada Muhimmancin zaman lafiya tare kuma da tunasantar da Shugabanni don samar da kyakkyawan shugabanci da zai magance matsalar tsaro da ke fuskantar sassa dabam- dabam na kasar nan.
Shi kuwa da yake nashi Jawabin ,Mataimakin shugaban yan Jarida na kasa Shiyar Arewa maso Yamma NUJ Zone A, wanda ya yi magana a madadin yan Jaridun ,Kwamarad Yusuf Idris, yace yan Jarida a shirye suke na ganin sungoyi bayan cigaba da mahukunta ke samarwa ga al’ummarsu , inda yayi kira da cewa kofar yan Jaridu a bude take na yayata abubuwa cigaba da Shugabanni ke samarwa al’ummumin su kasan cewar su dilka na hudu dake sa ldo don ganin cewa sauran ginshikan Gwamnati Uku da suka hada da bangaren Gwamnati,sashin Shari’a da kuma yin doka, sun sauke nauyin daya rataya a kansu na Samar na abubuwan mure rayuwa.
Daga Abdullahi Alhassan Kaduna.