Fadar shugaban ƙasa ta sanar da cewa, daga ƙarshen watan Janairu, dukkan kananan hukumomi a Najeriya za su fara karɓar kuɗaɗensu kai tsaye daga Kwamitin Asusun Bai Ɗaya na Gwamnatin Tarayya (FAAC), matakin da ke nuni da cikakken cin gashin kansu.
Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya bayyana hakan yayin wata hira da manema labarai. Ya kuma jaddada kudurin shugaban ƙasa Bola Tinubu na aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli na Yuli 2024, wanda ya bayyana cewa ikon jihohi kan kuɗaɗen kananan hukumomi ya sabawa kundin tsarin mulki.
Hukuncin ya kasance sakamakon karar da babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), ya shigar, inda ya nemi bai wa kananan hukumomi 774 damar cin gashin kansu. Sai dai, an ɗage aiwatar da wannan hukunci domin tabbatar da cewa an kammala shirye-shirye yadda ya kamata.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA X