Jami’an ƴan sanda sun kama wani ɗan ta’adda da ake masa lakabi da Likita a kan hanyar Akwanga jihar Nasarawa ya nufi garin Jos jihar Filato
Ƴan sanda sun cafkeshi akan mashin yana dauke da magazin na bindigar AK47 sama da 50 da kuma harsashin bindiga na AK47 sama da guda 200 zai kai jihar Filato
Likita ya bayyana cewa akwai sauran abokansa guda 6 suna dauke da kayan ta’addanci irin nasa, zasu kai garin Jos jihar Filato, yanzu haka yana tsare a ofishin ‘yan sanda na garin Akwanga
Me zaku ce akan wannan nasara da jami’an tsaron sukesamu?