Tawagar hadin gwiwar ‘yan sanda da sojoji da kuma’ yan banga a yankin sun kubutar da masu ibadar da aka sace a karamar hukumar Jibia da ke jihar Katsina.
‘Yan bindigar wadanda suka zo da yawa sun kewaye masallacin yayinda sukayita harbi a sama daka bisani suka sace su da sanyin safiyar Litinin.
Mai magana da yawun ‘yan sanda a Katsina, SP Gambo, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai yayin da ya bayyana nasarar da aka samu wajen kubutar da mutane 30 daga cikin 40 da aka sace.
A yayin faruwar lamarin, ‘yan sanda sun gudanar da bincike kai tsaye domin gano ainihin adadin saboda sun tabbatar da cewa mutane 10 sun bata ko da yake wasu na iya tserewa.
LIKE & FOLLOW US ON FACEBOOK & TWITTER