Iyalan waɗanda harin jiragen Sojin saman Najeriya ya rutsa da su a Zamfara sun nemi gwamnati ta biya su diyya da kuma tallafa wa waɗanda suka rasa iyayensu a harin.
Muhammad Aminu, ɗan uwa ga Babangida Ibrahim, wanda ya rasa ransa a harin, ya bayyana cewa waɗanda aka kashe su ne masu kula da iyalansu. Ya jaddada cewa wajibi ne gwamnati ta taimaka wa iyalan marigayun tare da ɗaukar nauyin maganin waɗanda suka jikkata.
A cewarsa: “Rashin daukar mataki daga gwamnati zai sa jama’a su daina goyon bayan yaki da ta’addanci a Najeriya.”
Malama Halima Idrisa, matar wani daga cikin waɗanda suka rasa ransu a harin jiragen Sojin saman ta koka cewa babu wata tallafa wa daga gwamnati bayan wannan mummunan lamari.
A martaninsa, mai bai wa gwamnan Zamfara shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mustapha Jafaru Kaura, ya ce bincike na ci gaba da gudana kan lamarin. Ya bayyana cewa an kafa kwamitoci biyu, ɗaya daga gwamnatin jihar da ɗaya daga rundunar sojojin sama, domin gano musabbabin abin da ya faru da kuma ɗaukar matakai masu dacewa.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA X