">
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
Saturday, October 18, 2025
No Result
View All Result
NEWSLETTER
Daily Episode Hausa
-18 °c
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
No Result
View All Result
Daily Episode Hausa
No Result
View All Result
">

Hukunce-Hukuncen Sallar Idi

by Abubakar Ismail kankara
May 10, 2021
in Uncategorized
0
Hukunce-Hukuncen Sallar Idi
Share on FacebookShare on Twitter
">

Daga S.P Imam Ahmad Adam Kutubi

 

A makon da ya gabata mun fara tabo darasin Zakkatul fidr, kafin mu shiga bayani a kan sallar idi, yana da kyau a san cewa,  Ita zakkatul fidr ya halatta a fitar da ita kafin kwana daya a yi sallah ko saura kwana biyu sallah, wani kaulin ma ta halatta ko da kafin kwana uku ne. Dan Annabi ya ce ita zakatul fidr tana kara tsarkake mai azumi da yawaita ladansa kuma ciyarwa ce da taiimako ga fakirai da miskinai wanda ya bada ita kafin zuwa masallacin idi to tana da ladan zakka cikakkiya kuma karbabbiya amma wanda ya bada ita bayan sauka daga sallar idi to sadaka ce daga cikin sadakoki. Wannan yana nuna mana ana son mutum yayi gaggawar fitar da ita kafin sallar idi, amma ko da bayan sallar idi ne bata fadi ba akan mutum sai dai idan bashi da abinyi kwata kwata to anan kam ta fadi akansa. Dan Allah yana cewa Bama daurawa rai abin da bata da iko akansa kuma Allah ya sake cewa kuji tsron Allah gwargwadon ikonku. An tanbayi annabi S.A.W akan ayar nan da take cewa hakika wanda ya tsarkake kansa ya rabauta ya kuma ambashi sunan Allah yayi sallah saboda shi. Annabi yace ai wannan aya ta sauka ne don tabbatar da zakatul fidr. Dan huzaima ya rawaito wannan hadisin.

Kamar yadda muka yi bayani a makon da ya wuce, ita zakkar nan sunnah ce mai karfi tana wajaba akan kowanne musulmi babba da yaro mace da namiji da ko bawa da sharadin akalla sa’i guda ya ragu daga cikin abincin da mutum ya mallaka a ranar data wajaba akansa. Yawanta sa’i guda ne akan kowanne mutum (Sa’i kuwa shine mudun nabiyi hudu ga kowanne mutum) lokacin take wajaba akan wanne mutum shine da faduwar rana, a yinin karshe na ramadan. A wani kauli kuwa ance bata wajaba sai wace garin sallah. Amma dai akowanne hali sunnah ne ayi saurin fitar da ita da fitowar alfijir na ranar sallah. Ana bada ita ga musulmi fakiri ko miskini, kuma ba’a bayar da ita ga bawa ko kafiri, da mawadacin mutum. Mutum shi zai fitar da zakkar nan ga wanda ciyar da shi tawajaba akansa da sababin zumunta ko aure ko bauta. Idan tawajaba akan mutum amma yayi jinkirin fitar da ita to bata faduwa akansa, saboda haka zai fitar da ita ko bayan watanni masu yawa. Baya halatta a fitar da ita sai daga daya daga cikin nau’in abincinnan;

RelatedPosts

Daga Aikatau Zuwa Mallakar Filaye: ‘Matan da ke Alfahari da Sauyin da Suka Samu’

Yan sanda a Kano Sun Gurfanar da Mutane 333 Da Aka Kama Lokacin Zaben Cike Gurbi a Kotu

Yadda Aka Gudanar da Aikin Gyaran Makabarta a Dala

Wani Magidanci Yayi Yunƙurin Kashe Kansa Tare da Yanke Al’aurarsa Sabida Matar Daya Saka Taki Amincewa Ta Dawo

  1. Alkama
  2. Sha’ir
  3. Sultu
  4. Dabino
  5. Zabib
  6. Cuku
  7. Gero
  8. Dawa
  9. Shinkafa
  10. Alasu
  11. Masara ko garin masara
  12. Wake
  13. Maiwa.

Amma idan an rasa daya daga cikin wadannan ya halatta a fitar da ita daga irin abincin da mutanen wajen suke ci.

 

Bayani A Kan Sallar Idi

Sallar idi sunnah ce mai karfi akan kowanne na miji baligi da mai hankali, ba matafiyi ba, kuma abarso ce bisa yara maza da bawa da matafiyi da tsohuwar da ba’a sha’awarta. Yawan sallar idi raka biyu ce. Babu bambanci tsakanin yarda akayi sallar idin karamar sallah data babbar sallah. Ga yadda akeyinta;   Tun farko mutum zaiyi niyyar koyi da liman Yace “Nayi niyyar koyi da liman acikin sallar idin kaza amma a boye a zuciyarsa ba’a bayyane  ba don fada a bayyane ba’a samu a shari’a. Daga nan liman zaice Allahu Akbar sau bakwai 7 acikin raka’a ta farko, tun kafin ya fara karatu. Kabbarar haramar sallar tana cikin guda bakwai din. Shi kuma mai bin liman zai fadi “Alllahu akbar” bayan fadan liman amma sau daya kawai kadai ake daga hannu sama wato a wajen kabbarar farko. Dakare kabbarorin nan sai liman ya karanci fatiha da surah a baiyyane amma amfison surar sabbi acikin raka’a ta farko. Sa’annan yayi ruku’u da sujjadai sannan ya mike tsaye don yin raka’a ta biyu. Zai ce Allahu akbar sau shida kafin ya fara karatu. Kabbarar mikewa tsaye tana cikinsu, zai karanta fatiha da sura a baiyya ne amma amfison karanta suratul shamsu a cikin raka’a ta biyu, sannan yayi rukuu’i da sujjadai, ya zauna yayi tahiya yayi sallama. Bayan kare sallah sai liman ya fuskanci jama’a yayi huduba biyu. Zai zauna a farkonsa da tsakiyarsa, zai fara kowace huduba da kabbarori kuma ya yawaita fadarsu a hudu barsa wato misali zai dinga cewa “Allahu akbar, Alllahu akbar, Allahu akbar” a lokacinnan dole ne wajibi ne mutane suyi shiru su saurari abinda yake fada a cikin hudubarsa.

 

Yadda Ake Gyaran Sallar Idi

Idan mutum ya samu liman yana tsakiyar karatu a cikin raka’a ta farko ko ta biyu sai yayi niyya ya bi shi ya fadi kabbarorin nan bakwai ko shi kadai, idan kuwa ya riga ya samu liman yayi wasu kabbarori sai ya bi shi ga sauran. Bayan liman ya cika nasa, shi kuma mai binsa sai ya kawo ragowar wanda bai samu yi da liman ba. Idan mutum ya taradda liman yana ruku’u  sai yayi niyya ya sunkuya ga ruku’u  danya same shi. Shikenan kabbarorin wannan raka’a sun fadi gare shi, babu komai akansa, sallah tayi kyau. Idan mutum ya samu raka’a ta biyu tare da liman, idan zai rama ta farko zaiyi mata kabbarorinnan nata bakwai 7. Idan imam ya kara wasu kabbara a bisa adadin da aka iyakancen bisa mantuwa, mai koyi dashi bazai fadi karinnan ba, idan liman ya rage kabbara daya ko abinda ya fi daya bai tuna ba sai bayan da yayi ruku’i to shi ma zaiyi sujjadar Kabli, idan kuwa kafin ruku’i ne sai ya fadi kabbarar sai ya sake karau daga farko to zaiyi kabbarar ba’adi. Idan mutum bai samu zuwa masallacin idi ba domin wani uzuri ko kuma dagangan to anaso yayi kabbarorinnan shi kadai.

Sunnonin Idi

Sunnah ne mutum ya rayar da daren sallah da yawaita ibada ga ubangiji Allah. Kamar sallar nafila da karatun alkur’ani da tasbihi. Kuma a ranar sallah abinso ne ga kowanne meusulmi babba da yaro mace dana miji mai zuwa masallacin idi da wanda baya zuwa yayi wanka, amfiso mutum yayi wanka tun da asuba wato bayan fitowar alfijir, kuma ana iya yinsa ko da bayan fitowar rana. Haka kuma abinso ne, ya sanya tufafinsa mafi kyau a ranar sallah. Amfison sababbin tufafi idan da hali, kuma abinso ne mutum ya tafi masallacin idi a kasa da gabobinsa, amma a wurin dawowa gida bayan kagama sallah zai iya hawa duk abinda yaga dama. Kuma abinso ce mutum ya sake sabuwar hanya a lokacin dawowarsa daga masallacin idi. Abinso ne ga wanda zai tafi masallacin idi yayi tayin kabbara tun daga fitowarsa daga gida har isarsa masallaci kuma yaci gaba da yin kabbarorin nan har sai lokacin da imam ya tashi yin sallah. Ga yadda kabbarorin suke “Allahu akbar, Allahu akbar, Allahu akbar, La’ilaha illallah, Allahu akbar, Allahu akbar, Walillahil hamdu”. Idan mutum bazai iya fadan dukan wadannan ba sai yayi ta Maimaita Allahu akbar, Allahu akbar ya isa. Kuma ba laifi yara suyi wasanni na farin ciki a ranar sallah.

">

Fadakarwa

Ba’a sallar nafila idan aka isa masallacin idi saboda itama nafilace sai dai ayita tasbihi har liman ya iso.

">

Wannan shi ne takaitaccen bayani a kan azumi da zakkar fidda kai da sallar idi daga littafin Alkalin Alkalai Alhaji Halliru Binji, mai sunaIbada Da Hukunci A Addinin Musulunci. Allah ya jikansa da gafara da mutanen gidansa da zuri’arsa da mu baki daya.

DAILY EPISODE HAUSA

LIKE & FOLLOW US ON FACEBOOK & TWITTER

Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail kankara

Abubakar Ismail Kankara is the founder and CEO of AIACCESS Contractors and the Managing Editor OF Daily Episode

Related Posts

Daga Aikatau Zuwa Mallakar Filaye: ‘Matan da ke Alfahari da Sauyin da Suka Samu’

Daga Aikatau Zuwa Mallakar Filaye: ‘Matan da ke Alfahari da Sauyin da Suka Samu’

by Yahuza Bawage
October 6, 2025
0

A wasu yankuna da ke kudancin jihar Kaduna a arewacin Najeriya, mallakar fili, musamman na noma, wani abu ne da...

zaben cike gurbi

Yan sanda a Kano Sun Gurfanar da Mutane 333 Da Aka Kama Lokacin Zaben Cike Gurbi a Kotu

by Abubakar Ismail kankara
August 18, 2025
0

Tun bayan kammala zaben cike gurbi da aka gudanar a fadin kasar nan, rundunar yan sandan jahar ta bayyana irin...

Yadda Aka Gudanar da Aikin Gyaran Makabarta a Dala

Yadda Aka Gudanar da Aikin Gyaran Makabarta a Dala

by Abubakar Ismail kankara
August 18, 2025
0

Duba da yadda rashin magudadan ruwa ke sanadiyar rubtawar kabaruruka musamman a lokutan damina, al’ummar unguwar Dala da kewaye dake...

yunƙurin kashe kansa

Wani Magidanci Yayi Yunƙurin Kashe Kansa Tare da Yanke Al’aurarsa Sabida Matar Daya Saka Taki Amincewa Ta Dawo

by Abubakar Ismail kankara
August 17, 2025
0

Rahotanni daga Jihar Borno sun bayyana cewa wani mutum mai shekara 50 da aka bayyana sunansa da Modu Isa ya...

Sarkin Rano Ya Haramtawa Iyaye Aurar da ’Ya’ya Mata Kafin Kammala Makarantar Firamare

Sarkin Rano Ya Haramtawa Iyaye Aurar da ’Ya’ya Mata Kafin Kammala Makarantar Firamare

by Abubakar Ismail kankara
August 16, 2025
0

A dai-dai lokacin da ake fama da yawan yaran da basa zuwa makaranta musamman a fadin arewacin kasar nan, mai...

Tsaro Ya Inganta

Kasa da Awa Ɗaya Bayan Ya Wallafa Cewa Tsaro Ya Inganta, ’Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shi

by Abubakar Ismail kankara
August 15, 2025
0

Rahotan da Daily Episode Hausa ta tattara daka jaridar idon mikiya na nuna da cewa, yan bindiga dake yawan kashe...

Next Post
Jami’an Tsaro Sun Ceta Masallata 30 Da Aka Sace A Katsina

Jami'an Tsaro Sun Ceta Masallata 30 Da Aka Sace A Katsina

Ko mutuwa nayi Zan roki Allah ya dawo Dani amatsayin dan fulani, mu fulani ba ‘yan ta’adda bane ~ Sarkin musilmi 

Ranar Alhamis Za A Yi Sallah — Sarkin Musulmi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

">
  • Talla
  • Tuntube Mu
  • Gida
TUNTUBE MU: 08032398985 info@dailyepisode.ng

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

Login to your account below

Forgotten Password?

Fill the forms bellow to register

All fields are required. Log In

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In